ECOWAS ta yi kira ga hukumomin Nijeriya da su hukunta wadanda ke da hannu a aikata laifin /Photo:Reuters

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta nemi a saki yara 80 da aka sace a Karamar Hukumar Tsafe da ke Jihar Zamfara a arewa maso yammacin Nijeriya.

A wata sanarwar da kungiyar ta fitar ranar Talata, ta yi tir da satar yaran inda ta yi kira ga hukumomin Nijeriya su hukunta wadanda suka aikata laifin.

Kazalika ta jajanta wa gwamnatin Nijeriya da kuma iyayen yaran da aka sace tana mai cewa za ta ci gaba da bayar da gudunmawa da Nijeriya ke bukata wajen yaki da ta'addanci.

A makon jiya ne wasu ‘yan bindiga suka sace yara akalla 80 a jihar Zamfara a lokacin da suka je yin ice da sanyin safiya.

“Kungiyar ECOWAS ta yi tir da wannan aikin ta’addancin kan yara kanana da ba su ji ba su gani ba kuma tana kira da a sake su cikin gaggawa ba tare da wani sharadi ba,” in ji sanarwar da ECOWAS din ta fitar.

Arewa maso yammacin Nijeriya na fama da matsalar garkuwa da mutane, da hare-haren 'yan bindiga.

Sai dai matsalar ta dan lafa kafin babban zaben kasar.

Gwamnatin Nijeriya ta sha fito da dabarun dakile garkuwa da mutane ciki har da hada katin shaidar dan kasa da layin waya da kuma takaita takardun kudin da ake amfani da su a kasar, amma lamarin ya faskara.

TRT Afrika da abokan hulda