ECOWAS  ta yi kira ga "hukumomin da suka kamata su yi gaggawar kammala tsare-tsare domin a sanya sabuwar ranar zaɓe."/Hoto: ECOWAS

Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta nuna matuƙar damuwarta game da matakin da shugaban Senegal ta ɗauka na ɗaga babban zaɓen ƙasar.

Ranar Asabar Shugaba Macky Sall ya sanar da ɗage zaɓen ƙasar wanda aka tsara gudanarwa a ranar 25 ga watan Fabrairun 2024.

Ya sanar da hakan a wani jawabi da ya yi wa ƙasar a Dakar babban birnin ƙasar inda ya ce an ɗage zaɓen sakamakon wasu matsaloli da ke tattare da jerin sunayen ƴan takara.

A Nuwambar bara ne Mista Sall ya saka ranar 25 ga watan Fabrairu a matsayin ranar zaɓen ƙasar inda ƴan takara 20 za su fafata a zaɓen sai dai a cikin mutanen babu sunayen wasu manyan ƴan adawa.

Sai dai a jawabin da Sall ya yi a ranar Lahadi, ya ce ya saka hannu kan wata doka wadda ta yi watsi da hanyar da aka bi wurin saka ranar a baya inda ya ce ƴan majalisa za su gudanar da bincike kan wasu alƙalai biyu dangane da martabarsu sakamakon suna da alamar tambaya a tattare da su ta fuskar zaɓe.

Sall ya sha nanata cewa zai miƙa mulki a watan Afrilu zuwa ga wanda ya ci zaɓe.

Bayan sanar da cewa ba zai yi takara ba a karo na uku, Sall ya bayyana Firaiminista Amadou Ba wanda ɗan jam’iyyarsa ne a matsayin magajinsa.

Kotun ƙasar ta cire sunayen gomman ƴan takara da zaɓen daga ciki har da ɗan adawar nan Ousmane Sonko da Karim Wade, ɗan gidan tsohon shugaban ƙasar Abdoulaye Wade.

Sanya sabuwar ranar zaɓe

A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ranar Asabar da maraice, ta bayyana "damuwa game da yanayin da ya sa aka ɗage zaɓukan" sannan ta yi kira ga "hukumomin da suka kamata su yi gaggawar kammala tsare-tsare domin a sanya sabuwar ranar zaɓe."

Kazalika ECOWAS ta yi kira ga dukkan 'yan siyasar Senegal su mayar da hankali wurin yin sulhu a tsakaninsu tare da haɗa kai wajen ganin an gudanar da sahihin zaɓe.

Haka kuma ƙungiyar ta jinjina wa Shugaba Salla bisa cika alƙawarin da ya ɗauka na ƙin sake tsayawa takara a zaɓen da ke tafe.

TRT Afrika