Ana asarar miliyoyin daloli sakamakon fashin teku a yankin Tafkin Guinea abin da shugabannin kasashen ECOWAS ke gani a kamata a dauki mataki. Hoto/ECOWAS

Shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS da ke raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka na gudanar da taro kan tsaron tekun yankin a Accra, babban birnin kasar Ghana.

Ana gudanar da taron ne ranar Talata karkashin jagorancin shugaban Ghana Nana Akuffo-Ado.

Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya, ya yi jawabi kan "matakan inganta zaman lafiya da tsaro a yakin da ake yi da laifukan da ke da alaka da fashin teku a yankin."

Ya ce ''Ya zama wajibi mu rika yin taruka na kungiyar kasashen yankin tekun Guinea" da zummar warware matsalolin fashin teku da ke addabar kasashen.

Tun da fari fadar shugaban Nijeriya ta bayyana cewa Shugaba Buhari zai nemi a yi hobbasa don magance matsalolin da suka dami yankin.

A sanarwar da fadar shugaban kasar ta wallafa ranar Litinin a Twitter, ta ce Shugaba Buhari zai bar Nijeriya ranar Talata domin halartar taron "shugabannin kasashe da gwamnatocin Yankin Tekun Guinea, (GGC) da Shugaba Nana Akuffo-Ado na Ghana zai shugabanta".

Ana asarar miliyoyin daloli da gomman rayuka sakamakon fashin teku a yankin Tafkin Guinea abin da shugabannin kasashen ECOWAS ke gani a kamata a dauki mataki.