Dubban jama'a a jihar Agadez da ke arewacin Jamhuriyar Nijar sun gudanar da zanga-zanga ranar Lahadi don neman sojojin Amurka su fice daga ƙasar.
Jihar Agadez nan ne Amurka take da babban sansanin jirage marasa matuƙa inda ta kashe kimanin $100m.
Masu gangamin suna ɗauke da kwalaye inda aka yi rubutu daban-daban da ke cewa "Nan Agadez ne ba Washington ba", "Sojojin Amurka, ku fita", da sauransu.
Masu zanga-zangar sun zargi Amurka da yin kaka-gida a Nijar duk kuwa da matakin da gwamnatin sojin ƙasar ta ɗauka na yanke hulɗar soji da ita.
Kazalika sun riƙe tutocin Nijar da Rasha inda suka riƙa yaba wa Shugaba Vladimir Putin kan alaƙar da ƙasarsa ta ƙulla da Nijar.
An gudanar da zanga-zangar ce ƙasa da mako biyu bayan an yi makamanciyarta a Yamai babban birnin ƙasar.
Haka kuma lamarin na faruwa ne jim kaɗan bayan Amurka ta amince ta kwashe dakarunta sama da 1,000 daga Jamhuriyar Nijar.
Mataimakin Sakataren Harkokin Wajen Amurka Kurt Campbell ne ya bayyana haka ranar Juma'a a ganawar da suka yi da Firaiministan Nijar Ali Mahaman Lamine Zeine a Washington.
Amurka tana amfani da sansanin sojin na yankin Agadez wajen yaƙi da ƙungiyoyin ƴan ta'adda da ke addabar yankin Sahel.
A watan jiya ne gwamnatin Nijar ta sanar da yanke hulɗar soji da Amurka, watanni kaɗan bayan dakarun Faransa sama da 1,500 sun kammala ficewa daga ƙasar.
Lamarin ya faru ne kwanaki kaɗan bayan wata tawagar jami'an gwamnatin Amurka, wadda ke ƙarƙashin jagorancin Mataimakiyar Sakataren Harkokin Wajen sashen Afirka, Molly Phee, ta je Nijar don ganawa da shugaban mulkin soji amma hakan ya gagara.
Gwamnatin mukin sojin Nijar ta zargi jami'an gwamnatin Amurka da rashin bin ƙa'idojin diflomasiyya da kuma ƙin gaya wa gwamnatin sojin ƙasar mutanen da ke cikin tawagar da ta je Nijar.
Sai dai bayanai sun ce gwamnatocin biyu za su ci gaba da gudanar da dangantakar diflomasiyya da ta tattalin arziki.
Sojojin Nijar sun kori Faransa daga ƙasar bayan sun samu rashin jituwa da ƙasar da ta yi musu mulkin mallaka, sakamakon juyin mulkin da suka yi wa Mohamed Bazoum a watan Yulin da ya gabata.
Kazalika sun soke yarjeniyoyi biyu kan harkokin tsaro da ƙasar ta ƙulla da Tarayyar Turai.
A watan Disamban da ya gabata sojojin na Nijar suka ƙulla yarjejeniya da Rasha. A makon jiya, sojojin Rasha da sauran ƙwararrun kan aiki soji guda 100 suka isa Yamai domin horar da dakarun ƙasar.