Dubban mutane ne suka taru a babban filin wasa na Yamai da ke Jamhuriyar Nijar domin nuna goyon baya ga sojojin da suka yi wa Mohamed Bazoum juyin mulki a makon jiya.
Mutanen sun yi gangamin ne ranar Lahadi yayin da wa'adin da kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka, ECOWAS ta bai wa sojojin su mayar da mulki hannun gwamnatin farar-hula yake cika.
Masu gangamin sun rika shewa da jinjina yayin da jagororin sojin da suka yi juyin mulkin na National Council for the Safeguard of the Homeland (CNSP) suka isa filin wasan mai wurin zaman mutum 30,000, da dama daga cikinsu rike da tutocin kasar Rasha da hotunan sojin da suka kifar da gwamnatin Bazoum.
Filin wasan, wanda ake kira Filin Wasa na Seyni Kountche, mutumin da ya soma yin junyin mulki a Nijar a 1974, ya cika makil da jama'a.
Janar Mohamed Toumba, daya daga cikin sojojin da suka yi juyin mulkin, ya gabatar da jawabi inda ya soki "mutanen da suka zura ido wadanda ke kitsa ganin faduwar kokarin Nijar na ci-gaba.”
"Muna sane da mugun nufinsu," in ji shi.
Da ma dai tun da safiyar Lahadi bayanai daga Yamai sun nuna cewa mutane na ci gaba da gudanar da lamuransu kamar yadda suka saba duk da cewa wa'adin da ECOWAS ta sanya wa sojojin don mika mulki ya cika a yau.
Ranar Lahadin da ta gabata ne kungiyar ta sanya wa Nijar takunkumai ciki har da rufe iyakokinta da kasar da katse wutar lantarki a yunkurinta na matsa lamba ga sojojin su koma bariki. Sai dai 'yan kasar ba su fasa gudanar da ayyukansu kamar yadda suka saba ba.
"Ban damu ba saboda na san cewa kimar ECOWAS ce za ta zube idan ta dauki matakan soji. Ba wannan ne burin shugabanninta ba," a cewar wata matar aure, Hadjo Hadjia, mai shekara 59, a hirarta da kamfanin dillancin labarai na Reuters a Yamai da safiyar yau.
Kawo yanzu dai ECOWAS ba ta yi bayani bayan karewar wa'adin da ta gindaya wa sojojin na Nijar.
Sai dai kalamanta a baya na kokarin yin amfani da karfin soji sun jawo muhawara sosai a yankin inda kasashe da kungiyoyi suka rika nuna adawarsu ga matakin.
Ranar Asabar da maraice, Aljeriya ta zama kasa ta baya-bayan nan da ta bayyana adawarta da yin amfani da karfin soji kan sojin da suka yi juyin mulki a Yamai.
"Amfani da karfin soji zai haifar da gagarumin rikici a duka yankin Sahel don haka Aljeriya ba za ta yi amfani da karfi kan makwabtanta ba," in ji wata sanarwar da ta ambato shugaban kasar Abdelmadjid Tebboune yana fitarwa a gidan talbijin na Ennahar, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Adawa daga cikin gida
Kazalika Shugaba Bola Tinubu na Nijeriya, wanda kuma shi ne shugaban ECOWAS, yana fuskantar adawa daga cikin gida game da shirinsa na tura dakarun kasar Jamhuriyar Nijar.
Ranar Asabar majalisar dattawan kasar ta yi watsi da bukatarsa ta aika sojoji Nijar. Maimakon haka, ta nemi ya ci gaba da amfani da hanyar lalama wajen shawo kan rikicin da Nijar ta fada a ciki sakamakon juyin mulkin da soji suka yi.
Daya daga cikin 'yan majalisar, Sanata Abdul Ahmed Ningi, ya shaida wa TRT Afirka cewa sun amince a dauki dukkan matakan da suka kamata a kan sojojin "amma ba za a je yaki da mutanen Nijar ba saboda dangantaka da ke tsakaninta da Nijeriya."
"Mun yi amannar cewa babu wata kasa da take da kusanci da dangantaka da Nijeriya kamar Nijar, don haka Sanatoci da yawa sun yi kalamai masu karfi na hana zuwa yaki," in ji dan majalisar dattawan ta Nijeriya.
Ita ma kasar Chadi mai makwabtaka da Nijar ta ce ba za ta yi katsalandan a batun juyin mulkin da aka yi a Jamhuriyar Nijar ba, kamar yadda Ministan Tsaronta Yaya Brahim Daoud ya bayyana a gidan talabijin ranar Juma'a.
Da ma dai tuni Mali da Burkina Faso suka yi fatali da yiwuwar tura sojoji Nijar, suna masu cewa hakan tamkar yin fada da su ne don haka za su mara wa sojojin Nijar baya.
Sai dai Faransa, tsohuwar uwar gijiyar Nijar, ta jaddada cewa a "tsaye" take don goyon bayan duk matakin da ECOWAS za ta dauka kan sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar.
"Makomar Nijar da zaman lafiyar yankin gaba daya suna cikin hatsari," in ji ofishin Ministar Harkokin Wajen Faransa Catherine Colonna bayan ta gana da firaiministan Njar da aka hambararar Ouhoumoudou Mahamadou, a Paris ranar Asabar.