An ji mutanen suna cewa "Tir da mulkin mallakar Amurka" da kuma "Tattakin 'yanta mutane na tafe"./Hoto: Reuters

Dubban masu zanga-zanga a babban birnin Nijar a ranar Asabar sun yi gangamin neman sojojin Amurka su bar kasar nan-take bayan gwamnatin mulkin sojin kasar ta ce ta janye daga yarjejeniyar soji da Washington.

Bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wa gwamnatin Mohamed Bazoum a watan Yuli, kasar ta Nijar a watan jiya ta bayyana cewa Amurka ce ta ƙaƙaba yarjejeniyar haɗin-gwiwar ɗin ta shekarar 2012.

Ɗalibai da wasu fitattun mutane a gwamnatin mulkin sojin ƙasar suna cikin ɗimbin mutanen da suka hallara a wajen majalisar dokokin ƙasar a Yamai.

An ji masu zanga-zangar suna cewa "Tir da mulkin mallakar Amurka" da kuma "Tattakin 'yanta mutane na tafe".

Korar Faransa

An kori dakarun Faransa a ƙarshen shekarar 2023, amma kimanin sojojin Amurka 1,000 sun ci gaba da kasancewa a birnin Agadez da ke arewacin ƙasar.

A ƙarshen watan Maris Nijar ta ce Amurka za ta mika wasu shawarwari na "raba" sojojinta daga ƙasar.

Washington ta ki cewa komai game da batun, amma ta ce ta tuntubi Nijar domin "samun karin bayani".

"Sun ce su (Amurkawan) za su tafi, saboda haka su tafi cikin lumana kuma da wuri," a cewar Sheikh Ahmadou Mamoudou, wani sanannen malamin addini .

Ƙona tutoci

An ga mutane riƙe da tutocin ƙasashen Burkina Faso da Mali da Nijar da kuma Rasha a yayin gangamin amma waɗanda suka shirya zanga-zangar sun ce a guji maganganun ɓatanci da zagi ga Amurka ko kuma kone tutocinta.

A watan Maris Nijar ta haɗa kai da makwabtanta Mali da Burkina Faso wajen kafa wata runduna ta haɗin gwiwa domin yaƙar waɗanda suka daɗe suna ta da ƙayar baya a ƙasashen uku.

Kasashen uku sun juya wa Faransa da ta yi musu mulkin mallaka baya kuma suka ƙarfafa dangantaka da Rasha.

TRT Afrika da abokan hulda