Ministan Sufurin Jiragen Sama na Nijeriya, Festus Keyamo, ya bayyana cewa Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa na shirin ɗage haramcin da ta saka wa Nijeriya na bayar da biza. Keyamo ya bayyana haka a wata tattaunawa da aka yi da shi ta tsawon mintuna 44 wadda aka wallafa a shafin YouTube na Fadar Shugaban Nijeriya.
Mista Keyamo ya bayyana cewa an cim ma matsaya tsakanin Shugaba Bola Tinubu da kuma Shugaba Mohamed bin Zayed Al Nahyan na Daular Larabawa a yayin da Tinubun ya kai masa ziyara a Satumbar 2023.
A lokacin ziyarar, an yi zaton cewa nan take za a ɗage haramcin, sai dai daga baya aka gane cewa ba nan take za a ɗage haramcin ba.
Keyamo ya ce duk da cewa Daular Larabawan a baya ta zayyana sharuɗan da za a cike kafin ɗage haramcin a hukumance, Gwamnatin Nijeriyar tuni ta kammala cike duk wasu sharuɗa waɗanda za su bayar da damar ɗage haramcin.
“Bayan wannan babbar tattaunawar, shugaban ƙasa ya sauƙaƙa mana abubuwa sosai, muna gode masa. Muna bin kadin lamarin a matsayinmu na ministocinsa. Mun yi iya bakin ƙoƙrinmu. Mun warware komai. Ku jira sanarwa daga gwamnatin UAE, kuma wannan sanarwar ta kusa," kamar yadda ya bayyana.
Keyamo ya bayyana cewa yana sane da ranar da Daular Larabawan za ta sanar da ɗage haramcin, amma ya ce ya rage ga gwamnatin ƙasar ta yi sanarwar.
Ana sa ran ɗage sanarwar za ta sauƙaka wa ‘yan Nijeriya zuwa Daular Larabawan a cikin sauƙi, da kuma ƙara yauƙaƙa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu.