Dakarun RSF na Sudan sun kashe farar hula ɗaya da jikkata 17 sakamkon harin da suka kai a Omdurman

Dakarun RSF na Sudan sun kashe farar hula ɗaya da jikkata 17 sakamkon harin da suka kai a Omdurman

Harin ya shafi fararen hula ne a lokacin da suke ɗebo ruwa daga wasu rijiyoyi da ke yankin Karari a cikin birnin.
Kawo yanzu dai babu wani karin haske daga ƙungiyar ta RSF game da wannan zargin. / Hoto: Reuters

Ma'aikatar lafiya ta kasar Sudan ta bayyana cewa, mutum daya ya mutu, wasu 17 kuma sun samu jikkata, sakamakon wani luguden wuta da kungiyar Rapid Support Forces (RSF) ta yi a garin Omdurman.

Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta kara da cewa harin ya shafi fararen hula ne a lokacin da suke ɗebo ruwa daga wasu rijiyoyi da ke yankin Karari a cikin birnin bayan harin da RSF ta kai kan madatsar ruwan Merow e Dam da kuma layin wutar lantarki na Omdurman, lamarin da ya janyo katsewar wutar lantarki.

A ranar Litinin din da ta gabata ce rundunar sojin Sudan ta sanar da cewa, wani hari da jiragen yakin RSF suka kai kan madatsar ruwan Merowe, lamarin da ya janyo katsewar wutar lantarki a yankuna da dama.

Kawo yanzu dai babu wani karin haske daga ƙungiyar ta RSF game da wannan zargin.

Rikicin da ke tsakanin sojoji da RSF, wanda ke gudana tun tsakiyar watan Afrilun 2023, ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 20,000 tare da raba mutane miliyan 14 da muhallansu, a cewar Majalisar Dinkin Duniya da hukumomin yankin.

AA