Yakin Sudan ya shiga wata na uku, kuma ya jawo mutuwar fiye da mutum 2,000. / Hoto: Reuters

Rundunar sojin Sudan SAF ta zargi rundunar bangaren adawa ta RSF da keta ka'idar yarjejeniyar tsagaita wutar da ta fara aiki a ranar Lahadi.

A wata sanarwa, rundunar sojin ta ce RSF ta kai hari yankin Tawila da arewacin Darfur a kwana biyu a jere, inda hakan ya sa ta kauce ka'idar yarjejeniyar tsagaita wutar da aka tsara cewa sai ranar Laraba da karfe 6 na safiyar kasar za ta zo karshe.

“'Yan tawayen sun kauce wa dokoki ta hanyar kai hari kan mazauna wajen tsawon kwana biyu, lamarin da ya jawo mutuwar mutum 15 da jikkatar gwamman fararen hula,” in ji rundunar sojin Sudan.

SAF ta kuma yi zargin cewa an raba daruruwan mutane da muhallansu a Tawila saboda kisan gillar da aka yi. Har yanzu RSF ba ta ce komai ba kan zarge-zargen.

Gwamnatocin Saudiyya da Amurka wadanda suka taimaka wajen cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Jeddah, har yanzu ba su ce komai ba kan batun.

Wata na uku

Kasashe biyun da ke shiga tsakani sun yi barazanar cewa ba za su ci gaba da jagorantar sasantawar da ake yi a Jiddan ba idan har bangarorin biyu suka yi biris da tsagaita wutar.

Yakin Sudan ya shiga wata na uku, kuma ya jawo mutuwar fiye da mutum 2,000 tare da raba mutum miliyan 2.2 da muhallansu, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Rundanar SAF, wacce shugaban riko Abdel Fattah al-Burhan ke jagoranta, da kuma ta RSF da Mohamed Hamdan Dagalo, ke jagoranta sun fara fada ne ranar 15 ga watan Afrilu, a yayin da Sudan ke shirin mika mulki ga farar hula bayan shafe shekara biyu sojoji na mulki.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce yakin ya yi muni, inda ake bukatar fiye da dala biliyan uku don aiwatar da ayyukan agaji.

Yakin ya lalata muhimman wurare kamar su asibitoci da makarantu da gine-ginen gwamnati.

TRT Afrika