Côte d'Ivoire ta dakatar da ƙungiyar ɗalibai bayan rasa rayuka da ke da alaƙa da rikici

Côte d'Ivoire ta dakatar da ƙungiyar ɗalibai bayan rasa rayuka da ke da alaƙa da rikici

Masu gabatar da ƙara sun ce ana tsare da mambobin ƙungiyar su shida bisa zargin kisan-kai da haɗin baki wajen aikata mummunan laifi.
Kungiyar daliban, Fesci, na da karfin fada a ji a jami'o'i. / Photo: AFP

Mahukunta a Côte d'Ivoire sun kama mambobin wata babbar ƙungiyar ɗalibai saboda ta'adddanci a jami'o'i, a wani ɓangare na binciken kisan-kai bayan an gano gawawwaki biyu na wasu shugabannin ƙungiyar adawa.

'Yan sanda da masu gabatar da ƙara sun kama mambobi shida na ƙungiyar ɗalibai ta Côte d'Ivoire (Fesci), ɗaya daga cikin ƙungiyoyin ɗalibai a ƙasar, tare da dakatar da dukkan ayyukanta.

Da yawan mutane a Côte d'Ivoire na fatan wannan mataki zai kawo karshen goyon bayan da Fesci ke samu, wadda ake zargi da cin karenta babu babbaka a jami'o'in Abidjan, birnin mafi girma a Côte d'Ivoire.

Mahukuntan sun dauki wannan mataki bayan kashe dalibai biyu Zigui mars da Aubin Deagoue da kuma mamban kungiyar adawa Sie Kambou da aka yi a karshen watan Satumba.

An gano gawarwaki

A daren 29 da 30 ga Satumba ne aka gano gawar Deagoue.

Sanarwar da gwamnati ta fitar ta ce wani bangare na kungiyar dalitai ta Fesci ne suka yi garkuwa da shi.

Bayan 'yan sanda sun fara gudanar da bincike, jami'an sun kama tare da tsare mutane shida, cikin su har da Kambuo.

Masu gabatar da karar sun ce ana tsare da mutane ne bia zargin kisa da aikata mummunan laifi da kisn kai.

Mutuwa ta biyu

Haka zalika ana tsare da mutane bisa zargin su da hannu a mutuwar Khalifa Diomande a watan Agusta, wanda dalibi ne kuma mamban Fesci.

Kungiyar daliban ce ta zama mai fada a ji a jamio'in Abidjan, in ji Wonswgue Silue, sakatatre janar na Kungiyar Dilaban Firamare da Sakandire ta Ivory Coast,

A yayin ganawar, ya ce "mambobinsu zau so su rungumi abin amagana ko kuma ku sha wahala."

Ya kara da cewar a bandakuna suna tursasa mutum buyayn CSA 100, kimanin CFA100 don buyan bukatarsu.

Ikirarin zaunci

A jami'ar Cocody da ke Abidjan, wani jami'in tsaro ya ce ya sha hana zaluntar mutanen da yake cin karo ana yi, kuma mambobin fesci ne ke yin zaluncin.

Wata rana da tsakar rana, fuskar na'ura mai kwakwalwa ta duki zafi, in ji shi, yana mai tunatar da yadda ake tare mutane tare da yi musu tsirara, ana dukan su.

Ya kara da cewa ba a daukar wani mataki bayan aikata wanan danyen aiki, kuma ya tabo batun magana ko rubutn da tushen labari ya nemi a boye sunansa.

A lokacinda ya kira dan sanda "Mutane ba sa magana saboda suna jin tsoro", in ji shi.

Zarge-Zargen fyade

Wani dalibi shi ma d aya nemi a biye sunansa ya bayyana yadda mambobin fesc suke tiursasawa dalibai mata su zama abokansu, amma AFP ba su gama tattabatar da wannan zargi ba.

Bayan AFP ta tuntube su, shugabanni da dama na Fesci sun ki cewa komai game ds wannan batu.

A shekarar 1990 aka kafa kungiyar Fesci wadda asali masu zanga-zanga ne da ke adawa da shugabancin jam'iyya daya a kasar.

Shugabanninta na farko sun hada da Firaminista na nan gaba, Guillaume Soro da Charles Ble Goude. Na farko ya zama na hannun daman Laurent Gbagbo, wanda ya zama shugaban kasa a tsakanin 2000 da 2010 lokacinda aka samu rikicin zabe.

'Na da karfi sosai'

An samu shugabannin fesci da hannu a rikicin zabe a tsakanin 2010 da 2011 inda aka kashe mutane sama da 3,000.

Da tafiya ta yi tafiya, kungiyar ta zama mai shiga tsakanin gwamnati da dalibau, in ji masanin kimiyyar siyasa Geoffroy Kouao.

"Ba za ka iya dabbaka wata manufa ta ilimi a Côte d'Ivoire ba, ba tare da Fesci ba", in ji shi inda ya bayyana ta da "Tana da karfi sosai".

Fesci na yi tasiri a wasu zabukan da ake yi, a kasar da daya bisa uku na jama'arta 'yan kasa da shekaru 35 ne.

Fesci ta bayyana cewar mambobinta ne ke da kashi uku na daliban Ivory Coast su 300,000.

Gidajen kwanan dalibai

Tana kuma shirya bayar da gidajen kwanan dalibai ta hanyar da ta saba wa doka, tana raba dakuna, fitar da kudade da kanta, in ji majiyar.

Tsawon lokaci, Ofishin da ke da alhakin ba wa dalibai wuraren zama bai yi aikinsa ba, kamar yadda dalibai da dama suka bayyana a tattaunawarsu da AFP.

Sun bayyana hakan a matsayin abu marar kyau da ke cike da rasahwa.

A farkon watan Oktoba, mahukunta sun kaddamar da aikin korar daliban da ke zaune a giudajen kwanan dalibai ba bisa ka'ida ba, tare da yin alkawarin sake bayar da dakunan.

Amma dalibin nazarin kimiyyar laifuffuka Franck - wanda AFP suka sauya sunansa sabod atsaro - na daga cikin wadanda suka koma wajen Fesci don samun dakin kwana, saboda sun ce ba su samu martani daga ofishin makaranta ba.

"Sun nemi da na biya CFA 10,000 a wata (kimanin dala 17) da kuma kudin da za a jje na CFA 200,000 (sama da dala 330)," in ji shi 0 ninki biyar ama da kudin da ofishin makaranta ke caja.

Da AFP ta tuntube shi, shugaban sashen bayar da dakuna ga dalibai na jam'ia ya ki cewa komai.

Masanin kimiyya Kouao ya ce an samar da Fesci ne sakamakon rashin nasarar tsarin jami'a a kasar.

Ya kara da cewa "Idan gobe, aka baiwa mafi yawancin dalibai gidajen zama, aka ba su kudade, idan babu dakuna darasi da suke cika makil da dalibai, idan muna d aiassun malamai, a bayyane yake karara cewa Fesci ba za su samu damar wani aiki ba, kuma kungiyar za ta mutu murus."

TRT Afrika