Kwararru suna dora alhakin wannan mummunan yanayi a kan tasirin sauyin yanayi/AA

Daga Charles Mgbolu

Shugabannin ƙasashen duniya suna taruwa a ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa UAE don halartar Taron Majalisar Dinkin Duniya kan Sauyin Yanayi karo na 28, wanda ake kira da (COP), da za a yi daga ranar 30 ga watan Nuwamba zuwa 12 ga Disamba.

MDD ta ce taron na COP28 wani muhimmin lokaci ne ga duniya don ta ɗauki mataki kan sauyin yanayi, inda ake sa ran sama da mutyum 60,000 za su halarci taron.

Mai masauƙin baƙi UAE ta ce COP28 zai kasance wata gagarumar hanya ta tattara bayanai kan ci-gaban da ta samu a Yarjejeniyar Paris.

Ana sa ran shugabannin ƙasashen Afirka za su gabatar da jawabai masu ƙarfi a wajen taron, musamman kan bayanan da suka tattara a yayin Taron Sauyin Yanayi na Afirka da aka gudanar a birnin Nairobi na ƙasar Kenya a watan Satumban da ya gabata.

Shugaban Ƙasar Kenya William Ruto ne zai jagoranci tawagar Afirka a matsayinsa na Shugaban Kwamitin Sauyin Yanayi na Ƙungiyar Tarayyar Afirka.

Ga wasu muhimman abubuwa biyar da ƙwararru ke fatan shugabannin Afirka za su sanya a cikin jawaban da za su gudanar a wajen taron.

Rage hayaƙin da masana'antu ke fitarwa a duniya

Afirka ta fi dfama da matsalolin da suka shafi sauyin yanayi da suka haɗa da fari da ambaliyar ruwa da ba a taɓa ganin irinsa ba, duk da haka kuma ita ce hayaƙin da masana'antu ke fitarwa ya fi yi wa illa duk da cewa ba ta fitar da shi sosai a yankunanta.

Bayyana cewa duniya na bukatar rage hayaƙi mai gurɓata muhalli daidai da ƙayyade dumamar yanayi zuwa digiri 1.5 bisa yarjejeniyar Paris abu ne da faɗar muhimmancinsa ba zai yi yawa ba.

Ana sa ran shugabannin Afirka a cikin jawabansu za su jaddada cewa ya kamata a cika daɗaɗɗen alkawarin da aka yi tun shekaru goma da suka gabata.

Ƙwararru sun jaddada cewa dole shugabannin Afirka su tunasar da mahalarta cewa nahiyar na ci gaba da shan wahalar matsalolin sauyin yanayi.

Gabanin taron na COP28, MDD ta ce a cikin ƙananan yara a ƙasashen Afirka 48 daga cikin 49 da aka tantance, an gano cewa suna cikin haɗari ko kuma matuƙar hadari na illar sauyin yanayi saboda yadda suke fuskantar annobar guguwa, da tsananin zafi, da sauran yanayi da bala'in gurɓata muhalli, da kuma samun dama ga muhimman ayyuka.

Ana sa ran shugabannin kasashen Afirka za su bayyana matsalolin nahiyar tare da matsa lamba kan manyan ƙasashen da suka fi fitar da hayaƙi mai guba da su ƙara ƙaimi wajen magance matsalar sauyin yanayi.

Sabunta alƙawurran sauyin yanayi

Shugaban COP28 Sultan Al Jaber ya ce zai yi matsin lamba sosai kan ƙasashen da suka ci gaba don samar da dala biliyan 100 a duk shekara na alkawarin da suka yi wa ƙasashe masu tasowa don magance matsalar da sauyin yanayi.

Ana sa ran shugabannin Afirka a cikin jawabansu za su jaddada cewa ya kamata a cika daɗaɗɗen alkawarin da aka yi tun shekaru goma da suka gabata.

A shekarar 2020, bisa bayanan OECD, ƙasashen da suka ci gaba sun ba da dalar Amurka biliyan 83.3 wanda bai kai yawan alkawarin da aka yi ba, kuma kashi takwas daga cikin kuɗaɗen ne kawai suka isa aljihun ƙasashe masu ƙaramin ƙarfi.

Ana sa ran shugabannin ƙasashen Afirka za su tunatar da ƙasashen duniya cewa, dole ne su jajirce wajen tabbatar da adalci, kuma ka da su bar kowa a baya, bisa ƙa'idojin adalci da daidaito.

Gyara tsarin ba da kuɗaɗen shawo kan sauyin yanayi

Majalisar Dinkin Duniya ta jaddada cewa gina gidaje masu jure wa guguwa da shuka amfanin gona masu jurewa fari da samar da ingantaccen ruwan sha, da saka hannun jari kan hanyoyin kare rayuwar jama'a na daga cikin muhimman abubuwan daidaitawa da ake bukata don rayuwa a duniya mai fama da sauyin yanayi.

Hakainde Hichilema shugaban kasar Zambia ya isa birnin Dubai domin halartar taron COP28. Hoto by Hakainde Hichilema

Kamar yadda suka jaddada a yayin Taron Ƙoli na Yanayi na Afirka karo na farko a Kenya, shugabannin Afirka a taron COP28 a Hadaddiyar Daular Larabawa na iya ƙara kira ga yin garambawul ga tsarin kuɗaɗen samar da yanayi na ƙasa da ƙasa.

Sun kasance suna neman a saka musu iyaka da saka su cikin tsarin samar da kuɗaɗe na gaskiya tare da kafa kariyar kudin waje saboda tsarin duniya na yanzu ya fi shafar kasashe masu karamin karfi da matsakaita (LMICs).

Sau da yawa suna ƙorafin cewa ba da lamuni na kasa da kasa galibi kan zo da kudin ruwa mai yawa na gajeren zango, lamarin da ke rage karsashin ci gaba da neman ababen more rayuwa da ya kamata su yi tasiri ga rayuwa a yawancin kasashen Afirka masu rauni.

Asusun Sauyin Yanayi

Tuni dai akwai kira daga MDD na sake dawo da Asusun Kula da Yanayi na Green a shekarar 2023. A zagayen farko na tattara albarkatun kasa, daga shekarar 2020 zuwa 2023, GCF ta tara dala biliyan 12.8 don inganta juriyar mutane biliyan a kasashe 128, a cewar rahoton MDD.

Ana ci gaba da zagaye na biyu don tallafawa GCF daga shekarar 2024 zuwa 2027, kuma ana sa ran shugabannin kasashen Afirka za su sake yin na'am da sanarwar Nairobi ga shugabannin kasashen duniya da su "ɗage bayan kudirin tsarin harajin carbon da ya hada da haraji kan cinikin man fetur."

A ba da tallafi, ba bashi ba

Kwararru sun bukaci shugabannin kasashen Afirka a wajen taron da su matsa ƙaimi wajen samar da ƙarin tallafi maimakon lamuni domin rage raɗaɗin bashin da ake fama da shi a nahiyar da kuma sauƙaƙa wa ƙasashen da ke fama da matsalar sauyin yanayi.

Wasu kasashen Afirka sukan karɓi lamuni daga cibiyoyin hada-hadar kudi da ke da sharuddan da galibi ba su dace ba.

Kwararru sun bukaci shugabannin Afirka da su jaddada cewa bai kamata nahiyar ta yi fama da bashin kudi don magance matsalar sauyin yanayin da ba ta taɓa ganin hakan ba.

TRT Afrika da abokan hulda