Gwamnatin Chadi ta yi watsi da wasu rahotanni da ke zargin sojojin ƙasar da kashe wasu masunta a Nijeriya da ke maƙwabtaka da ƙasar.
A cikin makon da ya gabata ne wasu mayaƙan sa kai a Nijeriya suka yi zargin cewa wani jirgin sojin Chadi ya buɗe wuta kan wasu masunta a Nijeriya inda ya yi zaton mayaƙan Boko Haram ne a yayin wani yunƙuri na ramuwar gayya.
A matsayin martani ga harin da 'yan Boko Haram suka kai kan sansanin sojin Chadi da ya yi sanadin mutuwar mutum akalla 40 a makon jiya, a ranar Larabar da ta gabata ne sojojin kasar Chadi suka kaddamar da wani hari ta sama a tsibirin Tilma da ke gundumar Kukawa a gaɓar tafkin Chadi a Nijeriya.
"Chadi na musanta wasu rahotanni dangane da hare-hare inda ake zargin sojojin kasar da kai hari kan fararen hula, musamman masunta a yankin tafkin Chadi," kamar yadda kakakin gwamnatin kasar Abderaman Koulamallah ya bayyana.
"Farmakin da aka kai zuwa yanzu ya faɗa ne kan wasu ƙungiyoyi waɗanda aka san da su," in ji shi.
Mai magana da yawun gwamnatin na Chadi ya jaddada cewa ayyukan da sojojin Chadi ke gudanarwa suna yin su ne "bisa tsari da ladabi kuma suna taka-tsantsan game da kai hari kan farar hula".
Sai dai wani sojin Chadi wanda ya buƙaci a sakaya sunansa ya tabbatar da batun hare-haren ga kamfanin dillancin labarai na AFP inda ya kuma ya ce akwai yiwuwar sojojin sun yi kuskure.
“Mayaƙan Boko Haram na yawan sajewa da masunta da manoma a lokacin da suke aikata laifuka. Hakan ne ya sa lamari ne mai wahala a rinƙa bambance tsakaninsu da ‘yan ta’adda,’ in ji shi.