Ministan Harkokin Wajen Faransa Jean-Noel Barrot ya tattauna da shugaban Chadi, Mahamat Idriss Deby a ranar Alhamis a N'Djamena.

Kasar Chadi ta sanar a jiya Alhamis cewa ta kawo ƙarshen wata yarjejeniya da Faransa da nufin ƙarfafa hadin gwiwa a fannin tsaro tsakanin kasashen biyu.

Sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen kasar ta fitar ta ce "Gwamnatin kasar Chadi na sanar da ra'ayoyin kasa da na duniya game da matakin da ta dauka na kawo karshen yarjejeniyar hadin gwiwar tsaro da aka kulla da kasar Faransa."

Sanarwar mai dauke da sa hannun Ministan Harkokin Wajen Ƙasar Abderaman Koulamallah, ta ce bayan shekaru da dama da kasar ta samu 'yancin kai, lokaci ya yi da kasar za ta "tabbatar da cikakken ikonta tare da sake ayyana kawancen abokantaka bisa manyan tsare-tsare na kasa baki daya."

Ta ce yanke shawarar soke yarjejeniyar da aka yi wa kwaskwarima a watan Satumban 2019, ko kadan ba ta nuna tabarbarewar alaka ta tarihi da danƙon zumunci a tsakanin kasashen biyu.

"Chadi ta ci gaba da kudura aniyar ci gaba da kulla kyakkyawar alaka tsakaninta da Faransa a sauran bangarorin da suka shafi moriyar kasashen biyu, domin amfanin al'ummomin kasashen."

Hukumomin kasar sun yi alkawarin mutunta tsarin da aka tanadar a cikin yarjejeniyar, ciki har da lokacin sanarwar, tare da hada kai da hukumomin Faransa don tabbatar da samun sauyi cikin sauki.

An sanar da matakin ne yayin da Ministan Harkokin Wajen Faransa Jean-Noel Barrot ya ziyarci kasar da ke yammacin Afirka.

Barrot, wanda ya isa N'Djamena babban birnin kasar a ranar Laraba, ya tattauna da shugaban kasar Chadi, Mahamat Idriss Deby a ranar Alhamis.

Tattaunawar tasu ta mayar da hankali ne musamman kan ayyukan bayar da agajin gaggawa a gabashin kasar sakamakon kwararar 'yan gudun hijirar Sudan da ke guje wa yaƙin da ake yi a kasarsu, da rikicin Sudan, da kuma fatan samun hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, in ji ofishin Shugaban Ƙasar a cikin wata sanarwa.

Chadi ta bi sahun sauran kasashen yankin Sahel da suka hada da Nijar da Mali da Burkina Faso wajen kawo karshen kawancen tsaro da kasar da ta yi musu mulkin mallaka.

A watan Agustan 2023 bayan hambarar da zababben shugaban kasar Mohamed Bazoum, shugabannin sojojin Nijar sun sanar da soke yarjejeniyoyin soji da suka kulla da Faransa yayin da suke ƙulla ƙawance da Rasha don samun hadin kan tsaro.

Wannan ya zo ne bayan da gwamnatin mulkin sojan Mali a shekarar 2022 ta ba da sanarwar ficewa daga yarjejeniyar tsaro da Faransa.

AA