Faransa ce ta kirkiro CFA a 1945 domin ta karbe iko da farashin kayayyakin da take samu daga kasashen da take mulka. Photo/AA

Daga Yasser Louati

A 1962 lokacin da Modibo Keita, sabon zababben shugaban Mali ya yanke shawarar samar da kudin Mali na Franc, kasashen da ke makwabtaka da kasarsa, wadanda mambobi ne na kasashe masu amfani da CFA, sun mayar da shi saniyar-ware a fannin hada-hadar kudi da tattalin arziki.

Bayan shekara guda, sojojin da Faransa ta horar sun halaka takwaransa na kasar Togo Sylvanus Olympio, bayan ya ayyana wani tsarin hada-hadar kudi mai zaman kansa na sabuwar kasarsa da ta samu ‘yancin kai.

Daga cikinsu akwai Etienne Gnassingbe Eyadema, mutumin da daga baya ya zama shugaban kasar Togo daga 1967 har zuwa mutuwarsa a 2005.

Faransa ce ta kirkiro CFA a 1945 domin ta samu ikon sanya ido kan farashin kayayyakin da take samu daga kasashen da take mulka da kuma kange kasashen daga tsarin hada-hadar kudi na kasashe rainon Birtaniya.

Sai dai ba kamar takwararta fam din Ingila ba da ta bace daga kasashen Afirka a tsakiyar karni na ashirin, har yanzu CFA shi ne kudin da ake amfani da shi a kasashe 14 na Afirka duk da ‘yancin kai da suke da shi daga kasar Faransa shekara da shekaru.

Kudin na CFA wadanda suka rabu kashi uku, kowane da nau’insa:

• Kudin CFA na Yammacin Afirka wanda Babban Bankin kasashen Yammacin Afirka ke samarwa ana amfani da shi a kasashen Benin da Burkina Faso da Guinea da Ivory Coast da Mali da Nijar da Senegal da kuma Togo.

  • Sai kuma CFA na tsakiyar Afrika da Babban Bankin kasashen yankin Tsakiyar Afirka ke samarwa ana amfani da shi a kasashen da suka hada da Kamaru da Tsakiyar Afirka, da Chadi da Equatorial Guinea da Gabon da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo.
  • Sai kuma CFA na kasar Comoros wadda kasar Comoros din kadai ke amfani da shi.

A duka wadannan nau’in kudaden, CFA din na ba Faransa damar kula da hada-hadar kudin a kasuwar duniya, da kuma tsayar da darajar kudin.

Haka kuma Faransa ce ke buga kudin sannan kashi 50 cikin 100 na baitul malin kasashen na kasar ta Faransa.

Rashin daidaito mai yawa da ke tsakanin tattalin arzikin Afirka da na Faransa, kwatanta kudaden yankin da kuma kudade masu karfi irin na Faransa a jiya da kuma euro a yau, dama yana da tasiri kai-tsaye ga tattalin arziki da kuma ci gaban kudaden CFA a Afirka.

Misalin haka ya hada da rage yawan kudi idan gwamnati na bukata, da tara da ake ci kan fitar da kaya, da rage gibin da ake da shi na manyan bankuna su saka baki.

Hakan yana sakawa su mayar da hankali kacokan kan yaki da hauhawar farashi.

Sai dai ga Faransa, batun karuwa ne kawai ake yi. Tsohuwar kasar mai mulkin mallaka na da hannu kan gudanarwar wadannan kasashen, inda take samun riba kan kasuwanci, ga shi kuma kudadensu na bankinta a ajiye wadanda za ta iya amfani da su a kasuwar hada-hadar kudi ta duniya.

Kamfanonin Faransa za su iya zuwa siyayya kasuwannin kasashen Afrika, su samu kayayyaki a farashi mai rahusa sa’annan su tura ribar kasarsu ba tare da fargaba kan cewa za a samu karyewa ko kuma karuwar darajar kudi.

A karkashin wadannan sharuddan, tambayar ita ce ta yaya kasa mai cikakken iko za ta zama tana da ‘yanci ba tare da an yi iko da yanayin hada-hadar kudinta ba?

Amsar wannan tambayar tana kan fitowar tsarin “daidaita” darajar kudi kan farashi daya, tun bayan fitowar CFA Franc, da kuma yadda kasashe hudu ne kawai cikin 15 da suke mambobin ke amfani da CFA suka balle daga yarjejeniyar.

Darajar CFA Franc ta sauya sau da dama a tsawon shekaru.

Misali a 1945, kudin Franc na Faransa na daidai da 0.588 na CFA.

Sai dai daga baya wannan farashin ya sauya a 1948 zuwa 0.5 da kuma 1960 lokacin da Faransa ta samar da sabbin kudinta inda farashin ya koma 0.2.

Sai dai lamari mafi muni yana gaba. A 1994, Paris ta yanke shawarar bitar tsayayyen farashin Franc na Faransa da kuma CFA.

Wani mugun mafarki shi ne wanda ‘yan Afirka suka ga shugabannin kasashensu suna saka hannu a kan wata yarjejeniya da aka yi a Dakar inda suka amince da matakin Faransa na karya darajar Franc da kashi 50 ya koma 0.01.

Hakan ya yi matukar illa ga nahiyar. Arzikin miliyoyin mutane ya karye inda kuma farashin kayayyaki da na shigo da su ya karu.

Zuwa wannan rana, abin da manyan bankunan nahiyar suke yi shi ne yaki da hauhawar farashi ta hanyar zuba jari ta hanyoyin da za a samu ci gaba.

Idan Faransa za ta iya karya darajar CFA da kuma tilasta matakinta kan shugabannin Afrika, su ma shugabanni za su iya da kansu su karya darajar kudadensu ta hanyar rage kashe kudi.

Daya daga cikin dalilan da Faransa ke fakewa da su kan CFA shi ne kudin na kawo daidaito a nahiyar Afirka.

Sai dai zuwa yanzu, nahiyar ba ta samu wani ci gaba ba, haka kuma kudin na bai-daya tsakanin kasashen 14 ya kasa zama wata babbar hanya ta cinikayya a tsakaninsu.

Darajar CFA Franc ta sauya sau da dama a tsawon shekaru.

Sai dai kamar yadda masanin tattalin arzikin Togo, Kako Nubukpo, ya bayyana cinikayya a kasashen da ake amfani da CFA ta kai kashi 10 cikin 100 a yankin Tsakiyar Afirka. Sai kashi 15 a yankin Yammacin Afirka wanda akwai gibi sosai idan aka kwatanta da kashi 60 cikin 100 na kasuwanci da ke yankunan da ake amfani da Euro.

Bugu da kari manyan kawayen kasuwanci na Faransa a Afirka sun hada da Morocco, mai kashi 18.9 cikin 100 na kasuwancin kasashen Afirka rainon Faransa.

Sai Aljeriya mai kashi 18.4 da Tunisia mai kashi 15.2 da Nijeriya mai kashi 8.5 da Afirka ta Kudu mai kashi 5.8. Babu ko daya daga cikinsu da ke amfani da CFA Franc.

Faransa ta yi nasara wajen rike ikon da take da shi kan batun hada-hadar kudi a kasashen da ta mulka sakamakon hadin kan da ta samu daga ‘yan boko na yankunan wadanda Faransa ta horas.

Misali, Sekou Toure ya ki yarda ya shiga kungiyar da Charles de Gaulle ya kafa a 1958, inda ya gwammace ya jagoranci jama’arsa su samu ‘yancin kai baki daya daga Faransa. Amma ya fuskanci matsi daga Faransa har ma da kasashen da ta rena a Afrika.

Tsohon abokin gwagwarmayarsa Felix Houphouet Boigny ya ninka barazanar da aka yi wa ministan harkokin waje na Faransa Bernard Cornut-Gentille, wanda ya ayyana cewa, “Idan Guinea ta ki amincewa ta shiga kungiyar kasashen renon Faransa, ba za mu ba ta garabasa ba,” in ji Boigny.

Boigny ya kasance minista ne karkashin mulkin De Gaulle kafin ya zama shugaban kasa na farko na Ivory Coast.

A lokacin, ya fito ya bayyana cewa “Ba wai Faransa kadai Guinea za ta fuskanta ba, za ta fuskancin sauran kasashe renon Faransa”.

Wannan barazanar ta fito a bayyane da wasu shirye-shirye domin lalata kasar, da kuma yunkurin jefa kasar cikin yunuwa inda har aka karkatar da jirgin ruwan shinkafa da kuma bayar da kudade na bogi duk don a durkusar da tattalin arzikin kasar, kamar yadda Pierre Mesmer ya bayyana, tsohon shugaban tattara bayanan sirri a wajen Faransa a kundinsa.

Duk da an shafe shekaru ana fama da talauci da kuma karancin ayyukan yi, shugabannin Afirka na yanzu sun yi kama da wadanda suka gabace su, wato suna daga baya. Ko matakin da aka fito da shi na sauya fasalin CFA ya fito ne daga shugaban Faransa.

A 2019, Emmanuel Macron ya kai ziyara Abidjan inda a gaban Shugaba Alassane Ouattara ya bayyana cewa: “Bayan na ji abin da matasanku ke cewa ne na fito da wannan tsarin.” “

Idan Macron yana so ya shaida wa shugaban Afrika cewa ba shi da amfani, da zai yi abin da ya fi haka. Idan wannan tsarin ya fito da sabon ‘yanci a takarda, yana bayar da wani kwaryakwaryan ‘yanci ne kawai na hada-hadar kudi.

“Eco” – wanda shi ne kudin da aka bayar da shawara na kasashen Yammacin Afirka – za a rinka kwatanta shi da euro. Sai dai har yanzu wannan yunkurin bai yiwu ba.

Tun daga samar da CFA Franc, ba a tanadi komai na kula da ita ba. Kin yarda a yi amfani da CFA da kuma batun da ake yi na kin amincewa da kula da hada-hadar CFA da Faransa ke kula da lamarin shi kansa ya tsufa kamar yadda ita kanta CFA din ta dade.

Thomas Sankara na Burkina Faso da Modibo Keita na Mali dukansu an kashe su ne da yi musu juyin mulki kuma mutanen da ke yi wa Faransa cikakkiyar biyayya ne suka maye gurbinsu.

Nuna alamomi ko kuma barin amfani da shi wani haramtaccen abu ne, daraktan kungiyar kasa da kasa ta La Francopho Kako Nubukpo, wanda dan kasar Togo ne ya rasa kujerarsa saboda nuna adawa da CFA.

Yadda Faransa ke kara bakin jini a Afirka da kuma yadda matasan wannan karnin ke tir da ita yana da alaka da yanayin kama-karyarta.

Babu wata mafita da Faransa ko Amurka ko China za ta bayar kan matsalolin Afrika. ‘Yan Afrika ne da kansu za su fito da hanyoyi domin farfado da nahiyarsu.

Togaciya: Wannan ra'ayi ne na mutum da ya rubuta makalar, ba lalle ba ne ya zama ra'ayin TRT Afrika.

TRT Afrika da abokan hulda