CBN ɗin ya kuma bayyana cewa zai rinƙa sakin waɗannan rahotannin a shafinsa na intanet . / Hoto: CBN

Babban Bankin Nijeriya CBN ya sanar da cewa zai dawo da wallafa muhimman rahotanni game da tattalin arziƙin ƙasar domin bayyana komai a fili.

CBN ya tabbatar da hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Talata inda ya jaddada ƙudurinsa na baje komai a faifai game da tattalin arziƙin Nijeriya.

Babban bankin ya bayyana cewa irin rahotannin za su ƙunshi bayanai game da kasuwanci na kamfanoni masu zaman kansu da hasashe game da tattalin arziƙi da yanayin hauhawar farashi.

CBN ya bayyana cewa sake dawowa da haɗa irin waɗannan rahotannin na daga cikin tsare-tsaren babban bankin waɗanda za su tabbatar da cewa jama’ar ƙasa da ‘yan kasuwa suna samun muhimman bayanai game da halin da tattalin arziƙin ƙasa yake ciki.

Babban bankin na Nijeriya ya ƙara da cewa zai riƙa wallafa waɗannan rahotanni a shafinsa na intanet www.cbn.gov.ng ta yadda za a iya samun duka bayanan.

Haka kuma CBN ya yi kira ga masana tattalin arziƙi da masu sharhi da masu zuba jari da kafofin watsa labarai da sauran jama’a kan su yi amfani da waɗannan rahotanni a matsayin sahihan bayanai game da tattalin arziƙin Nijeriya.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da tattalin arziƙin na Nijeriya ke tangal-tangal sakamakon hauhawar farashin kayayyaki da karyewar farashin naira da ma tashin dalar Amurka a ƙasar.

Wannan lamarin ya jawo babban bankin ya fito da tsare-tsare daban-daban domin farfaɗo da darajar nairar amma abin ya ci tura.

TRT Afrika