Babban Bankin Nijeriya CBN ya bukaci bankunan kasar da su soma tambayar kwastamominsu adireshinsu na shafukan sada zumunta.
A wata sanarwa da babban bankin ya fitar, ya ce ya dauki wannan matakin ne domin samar da karin matakan tantance kwastomomi ga cibiyoyin hada-hadar kudi a karkashin tsarin sa.
Haka kuma babban bankin ya ce wannan matakin yana daga cikin matakan dakile halasta kudin haram da daukar nauyin ta’addanci.
Baya ga adireshin shafukan sada zumunta, babban bankin ya bukaci bankunan kasar da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi da su kuma karbi adireshin e-mail da lambar waya da adireshin gida da sauran abubuwan da za su taimaka wurin tantance kwastoma.
Babban bankin ya kuma ce dole na kwastoma ya bayar da wata lamba ta tantancewa wadda ya samu daga gwamnati wadda ke jikin wani kati ko takarda mai dauke da suna da hoto da sa hannu.
Babban bankin ya bayar da misalin wannan kati ko takarda da fasfo ko katin dan kasa ko lasisin tukin mota.
Haka kuma babban bankin ya gargadi bankuna kan bude asusun ajiya wanda ba suna ko kuma yake na bogi ne.
A ‘yan kwanakin nan Babban Bankin Nijeriya ya yi ta daukar matakai ciki har da janye takunkumin da ya saka a baya kan iyakance kudin da kwastamomi za su iya cira a asusunsu na kudaden waje a bankunan kasar.
Haka kuma CBN din ya yi kokarin daidaita kasuwar bayan-fage da kuma farashin gwamnati ta hanyar karya darajar naira.