Majalisar ministocin Burkina Faso ta amince a tura dakaru don taimaka wa makwabciyarta Nijar, inda sojoji suka kifar da Shugaba Mohamed Bazoum a watan jiya.
Wata sanarwa daga majalisar ministocin kasar a ranar Laraba ta ce gwamnati ta amince a tura dakarun ko-ta-kwana Nijar "wanda ya yi daidai da tanade-tanaden kasarmu."
"Ba tare da sanya fargabar yaki a zukata ba, ya zama wajibi a fahimci cewa an dauki wannan mataki ne saboda kariya da kuma yaki da ta'addanci wanda wani abu ne da mutanen Burkina Faso ke so," in ji Ministan Tsaro Manjo Kanal Kassoum Coulibaly.
"Abin da ya shafi tsaron Nijar ya shafi tsaron Burkina Faso kai-tsaye."
A makon jiya gwamnatin sojin Nijar ta amince da karbar dakaru daga makwantanta Mali da Burkina Faso don taimaka musu "idan aka kai musu farmaki" bayan barazanar amfani da karfin soji da Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yankin Yammacin Afirka (ECOWAS) ta yi a kan Nijar a kokarin mayar da Shugaba Bazoum kan mulki.
Nijar ta fada rikicin siyasa ne a ranar 26 ga watan Juli lokacin da Janar Abdourahamane Tiani, tsohon shugaban dakarun fadar shugaban kasar Nijar ya jagoranci sojin mulkin da ya kifar da Shugaba Bazoum.
Shugabannin mulkin soji a Burkina Faso da Mali sun bayyana goyon bayansu ga gwamnatin sojin Nijar.