Burkina Faso da Nijar sun haramta nuna shirin talabijin na Faransa 'The Bachelor'

Burkina Faso da Nijar sun haramta nuna shirin talabijin na Faransa 'The Bachelor'

Sanarwar ta ce shirin "na nuna ƙyama ga matan Afirka, da rashin kare matasa, kuma ya saɓa wa dabi'u da al'adun kasar."
Sanarwar ta ce shirin "na nuna ƙyama ga matan Afirka, da rashin kare matasa, kuma ya saɓa wa dabi'u da al'adun kasar." / Hoto: AFP

Kasashen Afirka ta Yamma na Burkina Faso da Nijar sun haramta kallon wani shiri na gidan talabijin na Faransa saboda "cin mutunci" matan Afirka da kuma "saɓa wa dabi'u da al'adu" na ƙasashen biyu.

Wannan matakin dai ya yi daidai da matakin baya-bayan nan da kasashen biyu suka ɗauka - wadanda a baya Faransa ta yi wa mulkin mallaka - na haramta kallon kafafen yada labaran Faransa da dama.

Wata sanarwa da babbar hukumar sadarwa ta gwamnatin mulkin sojan Nijar ta fitar ta ce an umarci gidan rediyon Faransa Canal da ya daina watsa shirye-shirye ko sake nuna shirye-shirye a zango uku na shirin The Bachelor.

Sanarwar ta ce shirin "na nuna ƙyama ga matan Afirka, da rashin kare matasa, kuma ya saɓa wa dabi'u da al'adun kasar."

Ƙawancen Sahel

A ranar Laraba ne Nijar ta ba da umarnin haramcin.

Tare da Mali, Burkina Faso da Nijar na cikin mambobin kawancen kasashen Sahel da aka kafa a watan Satumban da ya gabata.

Kasashen uku sun fice daga kungiyar ECOWAS da ta yi barazanar shiga tsakani na soji a Nijar bayan juyin mulkin da aka yi a kasar a bara.

Tun daga wannan lokacin, kasashen uku suke aiki tare don yakar ta'addanci da hadewa a fannoni kamar samar da fasfo iri daya da sadarwa, da diflomasiyya.

TRT Afrika