Lauyoyin hambararren shugaban Nijar Mohamed Bazoum sun musanta zargin da sojojin kasar suka yi cewa ya yi yunkurin tserewa daga kasar.
Bazoum da iyalansa suna tsare a gidansa da ke fadar shugaban kasa a hannun sojojin da suka kifar da gwamnatinsa tun ranar 26 ga watan Yulin da ya gabata.
Ranar Alhamis sojojin sun ce tsohon shugaban Nijar da iyalinsa da masu dafa masa abinci da kuma wasu masu tsaron lafiyarsa sun yi "yunkurin tserewa daga Nijar".
An shirya daukarsu daga Yamai a jirgi mai saukar unguwa "mallakin wata kasar waje" domin kai su Nijeriya, a cewar kakakin gwamnatin sojin Amadou Abdramane a sakon da ya karanta a gidan talbijin na kasar.
Labari mai alaka: Mohamed Bazoum ya yi yunkurin tserewa — Sojojin Nijar
Ya kara da cewa an dakile yunkurin da suka yi na tserewa kuma an "kama manyan mutanen da suke da hannu a yunkurin da kuma masu taimaka musu".
Sai dai wani rukunin lauyoyin Bazoum ya yi watsi da babbar murya da wannan labari da "aka kitsa" kan tsohon shugaban kasar.
Ana tsare da Bazoum da matarsa da dansa ba tare da ba su damar ganawa da lauyoyinsu ba, kuma ba tare da sanin abin da duniya ke ciki ba, a cewar Mohamed Seydou Diagne, kakakin rukunin lauyoyin tsohon shugaban kasar, a wata sanarwa da ya aike wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
Ya kara da cewa sojojin da ke mulkin Nijar sun likitocin Bazoum ganawa da shi a yayin da ya kai musu abinci.
Diagne ya ce abokan huldar Bazoum ba su ji duriyarsa ba tun ranar Laraba da daddare zuwa Alhamis.
Ranar Juma'a shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana "matukar damuwa game da halin rashin tabbas" da Bazoum da iyalansa suke ciki.
A watan jiya, lauyoyin Bazoum sun gurfanar da gwamnatin sojin Nijar a gaban kotun ECOWAS kan yadda ake ci gaba d tsare shi ba tare tun da aka hambarar da gwamnatinsa.