Daga Abdulwasi'u Hassan
Abin da aka sani shi ne harshe yakan hada kan mutane. Amma akasin haka ne ya faru a Kamaru, inda amfani da Faransanci da Ingilishi ya haifar da rikicin da ya ki ci, ya ki cinyewa.
Rikici tsakanin bangarori biyu masu amfani da harshen Faransanci da kuma harshen Ingilishi ya janyo asarar rayuka 6,000, da tagayyarar kusan mutum miliyan daya a kididdigar kungiyar International Crisis Group.
Sabanin yawancin kasashen Afirka, Kamaru tana amfani da harsuna biyu sakamakon mulkin mallaka daga kasashen Faransa da Birtaniya.
Kasar Jamus ce ta fara yi wa Kamaru mulkin mallaka daga shekarar 1884 har lokacin da Jamusawan suka tsere a 1916, bisa tursasawar rundunonin sojin Faransa da na Birtaniya a Yakin Duniya na Daya.
Daga nan ne sai Faransa ta mulki mafi girman yankin Kamaru, wanda ya samu ‘yanci a 1960. Ita kuma Birtaniya ta mulki Kudanci da Arewacin Kamaru wanda suka samu ‘yanci a 1962.
Sai dai kuma, ganin cewa a lokacin Birtaniya tana mulkin mallaka a Nijeriya, an yi kuri’ar raba-gardama don fayyace ko yankin Kamaru da ke karkashinta zai hade da Nijeriya ne ko Faransa.
A sakamakon kuri’ar wadda Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar, yankin Arewaci ya zabi hadewa da kasar Nijeriya.
Amma yankin kudanci da ke karkashin Birtaniya ya zabi hadewa da Kamaru da ke karkashin Faransa.
Kasancewar yankin da ke amfani da Faransanci ya fi rinjaye, ya kankane mulkin kasar tun bayan samun ‘yanci. An bar yankin da ke amfani da Ingishi, wato kudu maso yamma da arewa maso yamma, suna korafin wariya.
A karshen shekarar 2016, rashin jituwar ta haifar da wasu kungiyoyin yankin, karkashin lauyoyi da malaman makaranta, shiga zanga-zanga da yunkurin ballewa don kafa Jamhuriyyar Tarayyar Ambazoniya a shekarar 2017.
’Yan awaren sun koka kan abin da suka kira tilasta musu amfani da Faransanci a makarantu, sai fannin shari' da gudanar da gwamnati. Akwai kuma koke kan rashin aikin-yi ga masu amfani da Ingilishi.
Nkongho Felix Agbor Balla, wani mai sharhi kan ‘yancin dan Adam ya nuna takaici kan adadin asarar rayuwa da rikicin ya haifar.
Ya fada wa TRT Afrika cewa, rikicin ya “hana yara zuwa makaranta, da janyo tawayar tattalin arziki, da satar mutane, da dauri ba bisa ka’ida ba, da kuma rushewar iyalai.
Me ya sa harshe ya zama silar rikicin?
Hajara Adamu, wata budurwa ce a Bamenda, wani gari a yankin na masu yin Ingilishi. Tana dab da rubuta jarrabawar kammala sakandire, sai rikicin ya barke a 2017.
Ta fada wa TRT Afrika cewa ala dole ta jira sai a shekarar 2020 sannan ta rubuta jarrabawar a Douala, wani birni a yankin masu Faransanci.
An rufe makarantu a yankin su Hajara, saboda ‘yan awaren suna garkuwa da ‘yan makaranta, da malamansu, don su tilasta daina halartar makarantu, inda ake amfani da Faransanci.
Sai dai kuma, ita Hajara, wadda shekarunta 20 tana magana da Ingilishi da kuma Faransanci, wanda ke nuna fuskoki biyu na kasar ta Kamaru.
Duk da a garin Bamenda ta girma, yankin da ake magana da Ingilishi, ta koyi Faransanci a firamaren da ta halarta a garin. Wannan ya sa tana sakin jikinta a duk inda ta samu kanta a fadin kasar.
Sai dai kash, ta ce wannan ba shi ne ke faruwa ga mafi yawan mazauna yankin da ke magana da Ingilishi, wadanda ba sa jin Faransanci ba.
Ta kara da cewa, “Mutanen da Ingilishi kawai suke ji, suna fuskantar bambanci”
‘Yan Kamaru suna da harsunan gargajiya da yawa, kamar Fula da Ewondo da Shuwa da kuma Arabiyya. Amma duka harsunan nan ba a faye jin sun haifar da rikici a kasar ba.
TRT Afrika ta ji ta bakin Sani Yola, wani dan asalin Nijeriya mazaunin Kamaru, wanda ya ce, “Rikicin nan da ake yi saboda bakin harsuna yana kona min rai!”
Sani Yola ya kara da cewa, “Za ka ga mutane masu kamanni daya, amma suna amfani da harshe daban-daban. Duk da cewa harsunan ba nasu ba ne, amma sun ba su wani muhimmanci mara iyaka.”
“Wadannan harsuna ba daga Afirka suke ba, amma su ne ke haifar mana da matsaloli,” in ji Sani.
Wani lauya mai kare hakkin dan adam, Nkongho Felix Agbor Balla, yana ganin, “rashin nazari da kyau” ne ke sa a yanke cewa silar rikicin na Kamaru matsalar harsuna ne.
Ya yi imanin cewa halayyar shugabanni a rikicin ce, da kuma tsarin hukuma, su ne suka fi tasiri a rikicin. Ya ce, “E, harshe yana daga cikin matsalolin. Amma ba shi ne babban batu ba.
Balla ya kara da cewa, “Mutane suna amfani da harshe wajen danniya kan wasu, kuma idan harshe ya bambanta ba sa mu’amalantar juna da kyau.”
A fahimtarsa, “Akwai matsalolin al’adu sannan akwai matsala mai dangantaka da tarihi. Duka suna da tasiri a rikicin.”
Bukatar zaman sulhu
A farkon wannan shekara, Canada ta sanar da cewa bangarorin rikicin sun nada ta ta zama mai shiga tsakani.
A wata sanarwa daga Ma’aikatar Harkokin Waje ta kasar, “Canada ta amince da wannan matsayi, a kokarinmu na inganta zaman lafiya da tsaro, da habaka dimukradiyya da ‘yancin dan adam.’’
Ministar Harkokin Waje, Melanie Joly ta ce: “Bangarorin da suka kulla yarjejeniyar su ne kasar Kamaru da Majalisar Mulkin Ambazonia, da Rundunar Tsaro ta Ambazonia”.
Sauran su ne “Kungiyar ‘Yantar da Mutanen Afirka, da Rundunar Tsaro ta Kudancin Kamaru, da Gwamnatin Rikon Kwarya, da kuma Gamayyar Tawagar Ambazonia. Bangarorin sun kuma bayyana fatan sauran kungiyoyi za su shigo tattaunawar.’’
Sai dai bayan wannan sanarwa ta kasar Canada, gwamnatin Kamaru ta sanar da cewa ba ta nemi wata kasa ta shiga tsakani ba.
A wata sanarwa, gwamnatin Kamaru ta ce, ba ta “amince da wata kasar waje ko hukuma da ke waje ba, ta shiga aikin shiga tsakani ba don warware rikicin.”
Sai dai kuma, a jawabinsa na sabuwar shekara, Shugaba Paul Biya ya ce gwamnatinsa a shirye take ta rungumi “hanyar lalama wajen warware rikicin ta amfani da sulhu da tattaunawa.’’
Yunkurin da aka yi a baya don warware rikicin duka sun gaza, bayan da kokarin kawo sulhu tsakanin gwamnatin tsakiya da ‘yan aware ta rushe.
Duk da haka, Mr Balla ya yi amanna cewa sulhu zai iya faruwa kuma ya kamata a gwada yin sa.
Ya ce, “Hanya mafi kyau don kawo karshen rikicin ita ce bangarorin biyu, da gwamnati da ‘yan tawaye su zauna su sadaukar da wasu bukatunsu don a daina kashe farar hula”.