Masu zanga-zanga suna riƙe da kwalaye da aka yi rubutu kamar "A kawo ƙarshen yunwa a Nijeriya", "A dawo da tallafin man fetur" da sauransu.

Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta aika da mutum 10 waɗanda ake zargi da hannu a zanga-zangar #EndBadGovernance zuwa gidan yari.

Mai shari'a Emeka Nwite na Babbar Kotun Tarayya ya aika da maza tara gidan gyaran hali na Kuje sannan ya aika da mace ɗaya zuwa gidan yarin Suleja.

Haka kuma alƙalin ya saka ranar 11 ga watan Satumba a matsayin ranar da zai yanke hukunci dangane da buƙatar bayar da belin da waɗanda ake zargin suka shigar a gaban kotun, kamar yadda gidan talabijin na Channels a Nijeriya ya ruwaito.

Aika su gidan yarin na zuwa ne bayan an gabatar da su a gaban kotu inda ake tuhumar su da cin amanar ƙasa da yi wa gwamnati bore da kuma yunƙurin hargitsa Nijeriya.

Mutum goman da aka gurfanar a gaban kotun sun haɗa da Michael Adaramoye da Adeyemi Abayomi da Suleiman Yakubu da Opaoluwa Simon da Angel Innocent.

Sauran sun haɗa da Buhari Lawal da Mosiu Sadiq da Bashir Bello da Nuradeen Khamis da kuma Abdulsalam Zubairu.

TRT Afrika