Babbar Kotun Tarayya a jihar Kano ta rushe dokar da ta sauke Sarki Aminu Ado Bayero tare da soke naɗin da gwamnatin jihar ta yi wa Sarki Muhammadu Sanusi.
Sai dai a hukuncin da Mai Shari’a Abdullahi Muhammad Liman ya yanke a yau Alhamis ya ce hakan bai shafi dokar da majalisar dokokin jihar ta yi wa gyaran fuska ba.
Kazalika kotun ta ce ta soke duk dokar da ta sauke sauran sarakunan jihar hudu na Rano da Karaye da Gaya da Bichi, a,,a dokar gyrana masarautun ta 2024 tana nan har sai na kammala sauraron shari'ar baki ɗaya.
Hukuncin kotun ya dogara ne da ƙarar da Aminu Babba Dan Agundi ya shigar gabanta a kan batun dokar rushe masarautu ta shekarar 2019.
Tun da farko mai shigar da ƙara Aminu Babba Dan Agundi ya bayyana wa kotun cewar rushe dokar da majalisa ta yi an tauye masa hakki.
Sai dai lauyoyin wadanda aka yi kara sun bayyana wa kotun cewar Aminu Babba Dan Agundi ba shi da wani hakki da majalisar ta tauye masa, sun kuma bayyana wa kotun cewar ba ta da hurumin sauraron shari’ar masarautu, don haka suka roki kotun ta yi watsi da karar.
Yayin da ya ke bayyana matsayarsa a yau Alhamis Mai Shari’a Liman ya kuma ayyana cewar umarnin da ya bayar tun da farko na cewar kowa ya tsaya a inda yake yana nan bai janye shi ba.
Mataki na gaba a yanzu kamar yadda lauyan mai ƙara ya faɗa shi ne alkali ya ce ya dakatar da shari'ar har sai an saurari ɗaukaka ƙara.
A watan Mayun 2024 ne Gwamnan Abba Kabir Yusuf ya bai wa Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II takardar kama aiki a matsayin Sarkin Kano, bayan da Majalisar Dokokin jihar ta amince da gyaran Dokar Masarautun jihar, sannan gwamnan ya sa mata hannu.
Jim kaɗan bayan hakan ne sai ɗaya daga manyan Hakiman Masarautar Kano Sarkin Dawaki Babba Alhaji Aminu Babba Ɗan Agundi ya shigar da ƙara kotu yana neman a hana gwamnati aiki da sabuwar Dokar Masarautun.
To sai dai a lokacin da yake jawabi bayan bai wa Sarki Sanusi takarda, Gwamna Abba Kabir ya ce umarnin da aka karɓo daga kotu ya makara.
“Na kafa hujja da cewa na sa hannu a kan Dokar Masarautar Kano da ƙarfe biyar na yamma, amma sai karfe biyu na dare wani ya zo ya ce wai wannan abin bai yi ba,” a cewar gwamna Abba.
“Mun sa hannu karfe 5:20, wai alkalin ma da ya ba da odar wai yana Amurka wai ya ba mu oda.”
Ya ƙara da cewa “Idan kuma akwai lauya da zai ce mana abin da muka yi ba daidai ba ne, mu ma muna da namu lauyan da zai ce daidai ne.”