Ba za a sake barin 'yan Faransa su sauka a Nijar ba: AFP

Ba za a sake barin 'yan Faransa su yi shawagi zuwa Nijar ba, a cewar wata sanarwa da majiyoyin kamfanonin jiragen sama suka fitar a ranar Alhamis.

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da takaddama tsakanin Paris da Yamai ke daɗa ruruwa bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar a bara.

"A cewar hukumomin Nijar, daga yanzu duk wani fasinja ɗan kasar Faransa ba shi da izinin shiga cikin kasar," in ji wata sanarwa ta cikin gida da Air Burkina ya fitar wadda AFP ya tattaro.

Sanarwar ta kara da cewa, "A sakamakon haka ba mu karbe su ba a cikin jiragenmu" zuwa Yamai babban birnin kasar.

Kazalika kamfanin jaragen sama na Royal Air Maroc shi ma ya yanke shawarar bin sabuwar dokar, sai dai ban da wadanda ke da shaidar ''izini na musamman'', a cewar wata majiya ta kusa da kamfanin.

Kamfanonin jiragen sama da dama da suke tashi zuwa Yamai wadanda suka hada da Ethiopian Airlines da Air Tunisie da Turkish Airlines ba su ba da amsa kai tsaye ba, yayin da kamfanin dillancin labaran AFP ya tuntube su.

Hukumomin Jamhuriyar Nijar ba su tabbatar wa kamfanin dillacin labaran Faransa AFP cewa ko an ayyana Faransa a matsayin wacce ba a maraba da zuwanta yakin Sahel da ke fama da talauci ba.

Tuni dai aka hana wasu ‘yan kasar Faransa shiga Nijar bayan da suka isa filin jiragen sama na Yamai a kwanan nan.

Dangantaka tsakanin Paris da Yamai ta kara tsami bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar 26 ga watan Yulin da ta gabata a Nijar, inda aka hambarar da zababben shugaban kasar Mohamed Bazoum.

Faransa ta rufe ofishin jakadancinta dake Yamai a watan Disamba bayan da aka umarci jakadan kasar Sylvain Itte ya fice daga Nijar.

Sojojin Faransa 1,500 na karshe da aka tura Nijar don yaki da masu yakin jihadi sun janye a ranar 22 ga watan Disamba.

A ranar litinin ne kungiyar tarayyar Turai EU ta caccaki Nijar kan kin ba da izini ga shugaban tawagar takaita rikicin farar hula na hukumar shiga kasar tare da bukatar a yi mata bayani kan dalilin wannan mataki.

A watan Disamba ne hukumomin Yamai suka yanke shawarar ba da umarnin fitar da tawagogi biyu na EU kan tsaro daga kasar, ciki har da EUCAP Sahel Mali da ke aiki a kasar tun shekara ta 2012.

Bayan fatattakar sojojin Faransa, gwamnatin sojin Nijar ta yi ta kokarin samun wasu sabbin abokai kana ta matsa kusa da kasar Rasha, wacce tuni ta shiga fagen harkokin soji da na siyasa.

Yamai dai na fama da tashe-tashen hankula biyu na masu ikirarin jihadi - wanda ya mamaye kudu maso gabashin Nijar, yakin dake makwabtaka da Nijeriya wanda ya dade yana fama da wannan matsala da kuma farmakin da mayaka da ke tsallakowa daga Mali da Burkina Faso suke kaiwa yammacin kasar.

Shugabannin sojojin kasar da ke kokawa kan tsadar kayayyakin abinci da karancin magunguna a sakamakon takunkumin da aka kakaba wa yankin, sun ce suna son a jira har zuwa shekaru uku kafin kasar ta koma mulkin farar hula.

Nijar ta hada kai da gwamnatin sojin Burkina Faso da Mali wajen sanar da ficewarsu daga kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afirka ECOWAS.

A tsakiyar watan Disamba ne, jagoran juyin mulkin Nijar Janar Abdourahamane Tiani ya ce al'amuran tsaro suna "ci gaba da daidaituwa" bayan wasu ''tarin nasarori" da sojojin suka samu wajen kwantar da tarzoma a yankin.

AFP