Gwamnan na Kano ya buƙaci hukumar yaƙi da cin hanci ta gudanar da bincike kan lamarin. / Hoto: Sanusi Bature

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ce ba shi da masaniya game da wata kwangila wadda ta shafi kai wa ƙananan hukumomin jihar 44 magunguna.

Gwamnan ya bayyana haka ne a sanarwar haɗin gwiwa da Kwamishinan Watsa Labarai na Kano Baba Halilu Dantiye da Daraktan Watsa Labarai na Gwamnatin Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa suka fitar.

Wannan sanarwa ta biyo bayan wani bidiyo da mai tonon sililin nan Bello Galadanci wanda aka fi sani da Dan Bello ya fitar inda yake zargin gwamnatin ta Kano da bai wa wani kamfani na Novomed kwangilar siyan magunguna.

A bidiyon, Dan Bello ya yi zargin gwamnatin Kano da bai wa ɗan uwan tsohon Gwamnan Kano Rabiu Kwankwaso kwangilar siyan magungunan inda ya ce a duk wata kowace ƙaramar hukuma ta Kano na bayar da naira miliyan tara ga kamfanin na Novomed mallakar Musa Garba Kwankwaso.

Sai dai a sanarwar ta gwamnatin Kano, gwamnan jihar ya bayar da umarni ga shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar kan ta gudanar da bincike nan take dangane da wannan zargin da kuma gabatar da rahoto game da hakan domin ɗaukar mataki.

Haka kuma gwamnan jihar ya buƙaci jama’ar Kano su yi haƙuri har zuwa lokacin da za a fitar da sakamakon wannan bincike.

TRT Afrika