Kamfanin man Nijeriya, NNPC, ya ce ba ya sayarwa ko hulɗa da gurɓataccen man fetur.
Wata sanarwar da babban daraktan watsa labaran kamfanin, Oluemi Soneye, ya sanya wa hannu, ta ce “ɓangaren NNPC da ke kula da gidajen man kamfanin ba ya hulɗa da gurbataccen man fetur domin yana biyayya ga ƙa’idoji da matakan tabbatar da inganci a ko wane matakin aikinsa domin tabbatar da cewa yana samar da man fetur mai inganci a gidajen mansa.”
Sanarwar ta biyo bayan fitowar wani faifan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta inda wani direba ya ce ya sayi gurɓataccan mai a wani gidan man NNPC dake kusa da wata babbar gada a Keffi, jihar Nasarawa.
Soneye ya ce ba zai yiwu a ce an sayi man daga gidan man NNPC ba domin gidajen kamfanin ba sa sayar da mai a galan-galan ko jarkoki.
“Mun gudanar da bincike a dukkannin gidajen manmu kuma mun tabbatar da cewa wannan iƙirarin ba gaskiya ba ne” a cewar daraktan watsa labaran NNPC .
Soneye ya buƙaci jama’a su yi watsi da zargin da ke cikin bidiyon yana mai ƙarawa da cewa masu yaɗa zargin da ba shi da tushe, ba sa kishin ƙasarsu.
Maganar gurɓataccen man fetur dai ya ja hankalin ƴan Nijeriya a lokacin da sabuwar matatar mai da attajirin Afirka, Aliko Dangote, ya gina ya yi iƙirarin cewa wasu na shigowa da man fetur mara inganci cikin ƙasar maimakon su sayi man fetur mai kyau daga matatar.
Nijeriya ta dade tana shigowa da man fetur tun lokacin da matatun mai mallakar ƙasar suka daina aiki duk da cewa ƙasar tana cikin ƙasashen da suka fi samar da ɗanyen mai a kasuwannin duniya.