“Tsohon shugaban ba shi ne mai filin da kansa ba domin filin wata gidauniya ce mai suna “Gidauniyar Muhammadu Buhari,” in ji Garba Shehu. .Hoto/Fadar Shugaban Nijeriya

Filin da Ministan Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, Nyesom Wike ya ƙwace da sunan Muhammadu Buhari, ba na tsohon shugaban ƙasar ba ne, in ji mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu.

A makon nan ne dai bayanai suka riƙa fitowa cewa Minista Wike ya sa an ƙwace filayen wasu manyan mutane da suka haɗa da Shugaban Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas da tsohon alƙalin-alƙalan Nijeriya, Walter Onnoghen da Sakataren gwamnatin Tarayya George Akume da kuma na wata Gidauniya mai suna Muhammadu Buhari.

Ministan ya ce ƙwace filayen ya zama wajibi ne saboda masu filayen ba su biya kuɗin shaidar mallakar filayen wato C-Of-O ba a lokacin da ya kamata.

Sai dai kuma kakakin tsohon shugaban ƙasar ya ce wannan filin da ala alaƙanta da gidauniyar Buhari ba na shi ba ne.

“Kamar komai da ke da alaƙa da Buhari—babu mamaki ko kaɗan a wannan ma—ana ta yayata magana a kafafen watsa labarai kan ƙwace fili da mahukuntan Birnin Abuja suka yi da iƙirarin cewa na tsohon Shugaba Muhammadu Buhari ne,” in ji sanarwar da Garaba Shehu ya fitar ranar Alhamis.

“Tsohon shugaban ba shi ne mai filin da kansa ba domin filin wata gidauniya ce mai suna “Gidauniyar Muhammadu Buhari,” in ji sanarwar.

Garba Shehu ya ce wasu makusantan shugaban ne suka kafa gidauniyar kuma sun bi ƙa’ida wajen kafa ta tare da tallafin abokan arziki.

“Amma sun fuskanci ƙalubale a ɓangaren filaye na Hukumar Birnin Abuja wadda ta nemi su biya kuɗi mai yawan gaske domin samun takardar shaidar mallakar fili, fiye da yadda ake ƙarba daga wurin ire-iren gidauniyar,” in ji sanarwar.

“Zai iya yiwuwa cewa wannan ba kuskure ba ne, an yi shi ne da gangan don haka ba abin mamaki ba ne da aka ƙwace filin cikin sauƙi,” a cewar Garba Shehu.

Sanarwar ta ce Buhari yana da fili ɗaya tilo a Abuja, kuma a lokacin da aka yi wa shi da ministocinsa tayin cika takardu domin samun filaye a Abuja, Buhari ya mayar da takardar ba tare da ya cika ta ba, yana mai cewa shi ya riga ya samu fili ɗaya a Abuja kuma kamata ya yi a bai wa waɗanda ba su da shi.

“Saboda haka ku gaya wa waɗanda suke ta tsalle-tsalle a kafafen sada zumunta suna tafka muhawara game da ƙwace filin Buhari a Abuja ko akasin hakan su kama gaskiya kuma su daina ɓata sunan tsohon shugaban ƙasar,” in ji Garba Shehu.

TRT Afrika