Kungiyar Tarayyar Afirka AU ta sanar da dakatar da Jamhuriyar Nijar daga dukkan abubuwa da ayyukan da suka shafi kungiyar da sassanta da cibiyoyinta.
AU ta fadi hakan ne a sanarwar da ta fitar ta bayan taron da ta gudanar ranar 10 ga watan Agusta a kan halin da siyasar Jamhuriyar Nijar ke ciki.
“An yanke shawara bisa amincewar dukkan sassan AU, musamman bisa Dokar AU ta Tsarin Mulki da Kwamitin Zaman Lafiya da Tsaro na AU da Sashen Dimokuradiyya da Zabuka da Sha’anin Gwamnati, da su yi gaggawar dakatar da shigar Jamhuriyar Nijar cikin dukkan wasu al’amura na AU da hukumomi da cibiyoyinta, har sai an mayar da kasar bisa turbar dimokuradiyya," in ji sanarwar.
Sanarwar ta kuma kunshi abubuwan da AU ta cimma da suka hada da yin nazarin halin tattalin arziki da zamantakewa da batun kai sojojin ko-ta-kwana zuwa Nijar tare da hada bayanai don bai wa hukumar.
Kazalika AU ta jaddada goyon bayanta ga ECOWAS da kokarinta na mayar da doka bisa kundin tsarin mulki ta hanyar diflomasiyya.
“A wannan mataki, muna neman dukkan kasashe mambobin AU da kasashen waje da suka hada da abokan hulda da su yi watsi da wannan sauyin gwamnati na Nijar su kuma guji yin duk wani abu da zai goyi bayan mulkin sojin Nijar,” a cewar AU.
Tun bayan da sojoji suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum ne kungiyoyi irin su ECOWAS da AU suka rinka yin barazanar daukar matakai a kansu ciki har da amfani da karfin soja.
Sai dai sojojin, tare da samun goyon bayan makwabtan Nijar, wato Mali da Burkina Faso, sun sha alwashin yin raddi mai karfikan duk wata barazana daga waje.
Batun Bazoum
Kungiyar Tarayyar Afirka ta kuma nanata bukatarta ta neman a saki Shugaba Mohamed Bazoum da sojojin juyin mulkin ke tsare da shit un bayan da suka hambarar da gwamnatinsa.
“A kuma saki sauran mutanen da ake tsare da su da girmama ‘yancinsu na ‘yan’adam da suka hada da kare lafiya da mutuncinsu.
“AU ta kuma yaba wa kokarin ECOWAS karkashin jagorancin Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, tare da yin kira ga kasashen ECOWAS da su tabbatar da takunkuman da kungiyar ta sanya wa Nijar.
“Sannan muna so ECOWAS ta dinga ba mu rahoto akai-akai kan ci gaban da ake samu ta fannin sanya takunkuman,” a cewar sanarwar AU.