By Charles Mgbolu
ART X, wanda wani biki ne wanda aka dauki lokaci ana gudanarwa a birnin Legas na Nijeriya ya kawo karshe, inda ya samu halartar daya daga cikin masu basira ta bangaren fasaha a Afirka da kuma wajen nahiyar.
A bana kadai, an samu masu fasaha sama da 120 daga kasashe 40 wadanda suka yi baje-kolin ayyukansu a dakunan ajiye kayayyakin 30.
Kamar yadda wadanda suka shirya taron suka bayyana, bikin ya bayar da dama ga masu fasaha masu tasowa su yi hulda da shahararru a bangaren irin su El Anatsui da Wangechi Mutu da Njideka Akunyili-Crosby da Yinka Shonibare CBE da kuma Hank Willis Thomas.
Wadda ta assasa taron Tokini Peterside-Schwebig a jawabinta a lokacin taron ta bayyana cewa wannan taron na takwas na da burin bayar da gudunmawa ga fasaha a Afirka da kuma waje.
“Biki ne na al’ada na musamman da ya wuce bikin al’adun gargajiya inda aka shafe kwanaki da dama ana abubuwa na fasaha,” in ji ta.
Tun bayan soma wannan taron a 2016, ART X ya bunkasa inda ya rika karbar bakuncin masu fasaha daga fadin duniya tare da yin fice kan irin shirye-shiryen da yake gabatarwa, wadanda suka hada da Art X Talks – wadda tattaunawa ce ta kai-tsaye.
Art X Live! ya kasance bikin wakoki na musamman wanda ake gudanarwa tsawon makon inda ake samun hadin kai da daya daga cikin masu fasaha wadanda suke tasowa da mawaka daga nahiyar Afirka da kuma gabatar da bayanai.
“Wuri ne wanda za mu bi diddigi kan mu su wane ne, da kuma inda za mu je nan gaba,” in ji Tokini.
"Ina son mutane su koyi rayuwa a wannan lokacin kuma su rika zama a cikin lokutan ta yadda za mu iya saka su a takardu,” in ji Chigozie Obi, wanda shi ne ya lashe gasar Art X a bana.
Akwai tsare-tsaren ci-gaba da dama a bangaren fasaha haka kuma akwai wuraren ajiyar kayayyakin fasaha da dama a yanzu, kamar yadda wani ma’ajin kayayyakin fasaha Daudi Karungi ya bayyana a wani taro.
Domin kara bayar da kwarin gwiwa ga masu fasaha da ke tasowa, ana shirya taro na musamman domin bayar da kyauta ga masu fasaha biyu wadanda ayyukansu suka fi kyau wadanda za su tafi gida da dala 10,000.