Sojojin Chadi da makiyaya sun kaɗa ƙuri’a a ranar Asabar a babban zaɓen da shugaban ƙasar ya bayyana a matsayin wani muhimmin mataki na komawa tsarin dimukuraɗiyya, amma jam’iyyun adawa suka ƙaurace wa zaɓen.
Mafi yawan al'ummar ƙasar ta yankin Sahel za su gudanar da zaɓen 'yan majalisar dokoki na ƙasa da na yankuna da na ƙananan hukumomi a ranar Lahadi daga karfe 6:00 na safe zuwa 5:00 na yamma.
Amma an gayyaci soji da kuma ƙabilun makiyaya don kaɗa kuri’a a ranar Asabar saboda dalilai na kayan aiki.
'Yan adawa sun yi watsi da zaɓen inda suka bayyana shi a matsayin na bogi.
"Babu yaƙin neman zaɓe, babu zaɓe a ranar 29 ga Disamba. Ku zauna a gida ku nemi wasu su yi hakan," kamar yadda babbar jam'iyyar hamayya ta Transformers ta wallafa a shafin Facebook tana aika saƙo ga masu kaɗa ƙuri'a.
Sojoji sun kaɗa kuri'a
Duk da haka, kusan kashi 45 cikin 100 na makiyaya 200,000 na ƙasar da sojoji 45,000 sun kaɗa ƙuri'unsu zuwa tsakiyar rana, kamar yadda ƙiyasin farko ya nuna.
Jami'an soji sun fara isa wata rumfar zaɓe da ke barikin Koundoul kusa da N'Djamena babban birnin ƙasar da wuri, kamar yadda kamfanin dillacin labarai na AFP ya gani.
"Ana ci gaba da kaɗa ƙuri'a kamar yadda aka saba. Sojoji na kaɗa kuri'a cikin 'yanci," in ji babban jami'in hukumar zaɓen Ousmane Houzibe.
An samu irin wannan fitowar ta jama'a a wani sansanin makiyaya da ke kusa da wani burtalin makiyaya.
“Makiyaya sun zo ne domin tambayar su waye za a zaɓa gobe, waɗanda za su inganta rayuwarsu,” in ji Sheikh Djibrine Hassabakarim, daya daga cikin wakilansu.
Zaɓen komawa dimukuraɗiyya
Ya ce sauyin yanayi ya sanya al’ummarsa cikin mawuyacin hali, tare da kashe dabbobi, da haifar da rikici da manoma, abin da ya sa suke shan wahala wajen ciyar da iyalansu.
Ana ci gaba da kaɗa ƙuri'a duk da hare-haren da ƙungiyar Boko Haram da ke ci gaba da kai wa a Yankin Tafkin Chadi, da kawo ƙarshen yarjejeniyar soji da Faransa, da kuma zargin Chadi da tsoma baki a rikicin da ya addabi maƙwabciyarta Sudan.
Gwamnatin Shugaba Mahamat Idriss Deby Itno tana gudanar da zaɓukan na ƙarshen mako a matsayin wani muhimmin mataki na komawa tsarin dimukuraɗiyya.
Mahamat Deby mai shekaru 40 ya karɓi mulki a shekarar 2021 bayan mutuwar mahaifinsa Idriss Deby Itno wanda ya shafe shekaru 30 yana mulkin kasar ta yankin Sahel.
Mahamta ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekaru biyar a watan Mayun da ya gabata.
Tun shekarar 2011 ba a sake zaɓen 'yan majalisa ba a ƙasar.
An yi ta ɗage zaɓuka da dama tun daga nan saboda barazanar tsaro da matsalolin kuɗi da annobar korona.