Ofishin kare hakkin ɗan'adam na Majalisar Ɗinkin Duniya ya fitar da wani sabon rahoto ranar Juma'a, inda ya nuna yadda aka riƙa lalata da mutane, ciki har da fyaɗe a yaƙin d ke faruwa yanzu haka a Sudan, yana mai cewa hakan ka iya zama laifin yaƙi.
Sudan ya faɗa cikin rikici a tsakiyar watan Afrilu lokacin da aka samu rashin jituwa a Khartoum tsakanin sojojin ƙasar da ke ƙarƙashin Janar Abdel Fattah Burhan, da dakarun Rapid Support Forces, da ke ƙarƙashin mataimakinsa Janar Mohammed Hamdan Dagalo.
Nan da nan rikicin ya rikiɗe zuwa yaƙi inda ya bazu zuwa sassan ƙasar, musamman birane da kuma yankin Darfur mai fama da rikici, kuma ya zuw yanzu a yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 12,000 sannan ya raba fiye a mutum miliyan 8 da muhallansu, a cewar rahoton.
Rahoton, wanda ya mayar da hankali kan abubuwan da suka faruwa daga watan Afrilu zuwa 15 ga watan Disamba, ya fito da irin ɓarnar da aka tafka da kuma cin zarafin da aka yi wa mutane, musamman a ƙasar da ƙungiyoyin kare hakkin ɗan'adam suka juya wa baya sakamakon yaƙin da ke faruwa a Gaza da Ukraine.
Rahoton ya gano cewa an yi lalata da mutum aƙalla 118, ciki har da fyaɗe — inda aka ɗora alhakin wannan ta'ada kan dakarun sa-kai na rundunar RSF waɗanda rahoton ya ce suna yi wa mutane fyaɗe a gidaje da kan titi.
MDD ta ce ‘’An tsare wata mata a cikin wani gini inda aka yi ta mata fyaɗe a-kai-a-kai har tsawon kwanaki 35."
Kazalika rahoton ya yi nuni kan yadda ake ɗaukar yara ƙanana aikin soja a ɓangarorin biyu da ke rikici da juna. "Wasu daga cikin waɗannan take hakki za su iya zama laifuffukan yaki," in ji babban jami'in kare hakkin ɗan'adam na Majalisar Ɗinkin Duniya, Volker Türk, yana mai kira da a gaggauta gudanar da bincike mai zaman kansa kan zargin cin zarafi da take hakki.
Rahoton ya dogara ne kan hirar da aka yi da mutane sama da 300 waɗanda abin ya shafa da kuma shaidu a ƙasashen Habasha da Chadi da ke maƙwabtaka da Sudan inda akasarin ƴan ƙasar suka tsere, tare da nazari kan hotuna da bidiyo da hotunan tauraron ɗan’adam daga yankunan da ake rikici. Irin ɓarnar da yaƙin yake haifarwa ta zarce lokacin da aka gudanar da wannan bincike, in ji MDD.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta kafa hujja kan wani bidiyo da ya yaɗu a makon jiya daga jihar Kordofan ta Arewa da ke ƙasar inda aka nuna wasu mutane sanye da kakin sojojin Sudan ɗauke da yankakkun kawunan dakarun ɓangaren da ke adawa da su.
“Kusan shekara ɗaya yanzu, labarin da ke fitowa daga Sudan bai wuce kan batun mutuwa ba da wahalhalu da ƙunci sakamakon rikice-rikice marasa ma’ana da take hakkiln ɗan'adam da cin zarafi da ke faruwa babu ƙaƙƙautawa,’’ in ji Turk.
“Dole ne a daina harba bindigogi, sannan a kare fararen-hula,” in ji shi.
Da yake magana daga birnin Nairobi na ƙasar Kenya ta manhajar bidiyo ga taron Majalisar Ɗinkin Duniya da ke gudana a Geneva a ranar Juma’a, Seif Magango, mai magana da yawun ofishin kare hakkin ɗan’adam na yankin ya ce “mutanen da suka rasa matsugunansu a Sudan sun zarta miliyan 8 ya zuwa yanzu."
A farkon watan Fabrairu, Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, António Guterres, ya shaida wa manema labarai cewa, babu wata hanyar soji da za ta magance rikicin Sudan, ya kuma buƙaci manyan hafsoshin ƙasar su fara magana kan kawo ƙarshen rikicin.
Guteres ya jaddada cewa ci gaba da faɗa “ba zai kawo wata mafita ba don haka dole ne mu dakatar da hakan.”