An dauke tsohon shugaban Sudan Omar al-Bashir daga babban birnin kasar Sudan da yaki ya daidaita zuwa garin Merowe da ke arewacin kasar domin kula da lafiyarsa, kamar yadda lauyansa ya bayyana.
Lauya na sa Mohamed Hassan al-Amin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa an kai tsohon shugaban mai shekaru 80 wani wurin da ake tsare da shi a Merowe kafin a yi masa magani a wani asibiti a garin.
"Yana bukatar a duba lafiyarsa da kuma duba lafiyarsa lokaci-lokaci. Wani lokaci yana samun wasu matsaloli, wanda ke bukatar bin diddigi. Amma yanayin da yake ciki ba mai tsanani ba ne a yanzu," in ji Amin.
Ya kara da cewa, har yanzu ba a gano abin da ke damunsa ba, kuma za su iya bukatar magani a wata kasa a wajen Sudan, yana mai cewa wannan shi ne karon farko da aka dauke Bashir daga babban birnin kasar.
Laifin almundahana
An samu Al Bashir da laifin cin hanci da rashawa da almundahana da kudade ba bisa ka'ida ba, sannan kuma ya fuskanci wasu shari'o’in kafin yaki ya barke a watan Afrilun 2023.
An tsare shi a baya-bayan nan a wani sansanin soji da ke Omdurman, wani yanki na babban birnin kasar Sudan inda sojojin suka ja tunga a yakin da suke yi da dakarun Rapid Support Forces (RSF).
An gabza kazamin fada a Omdurman, kuma RSF ta yi ruwan bama-bamai a unguwannin birnin ranar Talata, in ji wasu shaidu uku.
Rikicin bai shafi Merowe mai tazarar kilomita 340 ba a arewa
Wanda ICC ke nema
Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Kasa da Kasa (ICC) na neman Al Bashir bisa zargin aikata laifukan yaki da laifukan cin zarafin bil'adama da kuma kisan kare dangi da suka shafi rikicin da ya barke a Darfur daga shekara ta 2003.
Shi ma wani tsohon minista Abdelrahim Mohamed Hussein da ke fuskantar sammacin ICC, an mika shi kai shi Merowe tare da Bashir don kula da lafiyarsa, a cewar Amin.
Haka shi ma wani tsohon babban jami'i, Bakri Hassan Saleh, daya daga cikin makusantan Bashir a tsawon shekaru talatin da ya yi yana mulki, tuni aka kai shi asibitin Merowe.