Aƙalla 'yan sanda 35,000 rundunar 'yan sandan Nijeriya ta aika jihar ta Edo. / Hoto: INEC

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta sanar da tsawaita lokacin kada kuri’a a zaben gwamnan jihar Edo da ke ci gaba da gudana.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, Mohammed Haruna, kwamishinan INEC na kasa kuma mamba a kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a, ya ce za a jefa ƙuri’a a rumfunan zabe da ba a fara kada kuri’a da wuri ba.

Haruna ya ce karin wa’adin zai bada damar kada kuri’a har sai duk wadanda suka cancanta da suka isa rumfunan zabe da karfe 2:30 na rana sun kada kuri’unsu.

Tun da safiyar yau dubban mutane suka fita zuwa rumfunan zaɓe a faɗin jihar domin kaɗa ƙuri’a a zaɓen gwamnan Jihar Edo da ke kudancin Nijeriya.

‘Yan takara 17 ne waɗanda suka haɗa da maza 16 da mace ɗaya ke fafatawa a zaɓen domin neman maye gurbin gwamna mai ci a halin yanzu wato Godwin Obaseki.

Sai dai daga cikin ‘yan takarar 17, mutum uku ne za a iya cewa za su fi fafatawa a tsakaninsu.

‘Yan takarar ukun waɗanda suka fi shahara sun haɗa da Asuerinme Ighodalo na Jam’iyyar PDP sai Monday Okpebholo na Jam’iyyar APC da kuma Olumide Osaigbovo Akpata na Jam’iyyar Labour Party.

A wannan zaɓen wanda ake gudanarwa a ƙananan hukumomi 18 na Jihar Edo, mutum miliyan 2.2 ne suka cancanta su jefa ƙuri’a, kamar yadda hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta tabbatar.

Rahotanni sun tabbatar da jibge jami’an tsaro masu ɗumbin yawa a jihar waɗanda suka haɗa da sojoji da ‘yan sanda da jami’an NSCDC musamman a Benin City babban birnin jihar.

Jami’an ‘yan sandan Nijeriya sun tabbatar da aika ‘yan sanda 35,000 jihar domin tabbatar da tsaro, haka kuma ‘yan sandan sun tabbatar da aika jirage marasa matuƙa da helikwafta da sauran kayayyakin aiki domin taimakawa a wurin tabbatar da tsaro a yayin zaɓen.

TRT Afrika