Wata mai magana da yawun ‘yan sanda ta ce rikicin na da alaƙa da harajin kamfanin man fetur da ke yankin kuma an tabbatar da mutuwar mutum 10. Hoto: Others

Aƙalla mutum 19 ne ake fargabar sunr asa rayukansu bayan wani mummunan rikici da ya faru tsakanin wasu ƙungiyoyi biyu da ke gaba da juna a ƙarshen makon da ya wuce a jihar Rivers da ke kudancin Nijeriya, kamar yadda kafafen watsa labaran yankin suka rawaito.

Faɗan ya ɓarke ne a ranar Lahadi lokacin da ‘yan bindiga da ake zargin na ƙungiyar asiri ne suka far wa al’ummar Obelle a jihar a matsayin ɗaukar fansa, bayan da suka suka kai musu harin farko a ranar Laraba har suka kashe mutum bakwai, in ji jaridar Punch.

Wata mai magana da yawun ‘yan sanda ta ce rikicin na da alaƙa da harajin kamfanin man fetur da ke yankin kuma an tabbatar da mutuwar mutum 10.

An yi amannar cewa ɓangarorin da ke rikici da junan mambobin ƙungiyoyin Icelanders da Deybam ne, in ji jami’ar ‘yan sandan, inda ta ƙara da cewa ana cigaba da bincike amma ba a kai ga kama kowa ba tukunna.

Mazauna yankin sun ce ɓangarorin biyu na fitattun ƙungiyoyin asiri ne da ke faɗa a kan samun iko, da gabarsu ta dawo ɗanya sharaf a baya bayan nan bayan da aka shafe fiye da shekara biyu da lafawar rikicinsu.

Amma wasu ganau sun ce abin ya haɗa da rasa rayukan wasu da ba su ji ba ba su gani ba a faɗan.

AA