Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya ce bai kamata a daga kafa ga masu tayar da yamutsi a jihar Filato ba. /Hoto:Rundunar Sojojin Nijeriya

Shugaban rundunar sojoji kasa ta Nijeriya Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya bayar da umarni ga dakaru na musamman da ke wanzar da zaman lafiya a jihar Filato su gaggauta kawar da 'yan ta'adda da suka addabi karamar hukumar Mangu.

Ya bayar da umarnin ne a yayin da yake jawabi ga hadin-gwiwar dakarun Runduna ta 3 da Rundunar Operation Safe Haven ranar Asabar lokacin ziyarar da ya kai jihar Filato mai fama da rikice-rikicen kabilanci da na addini.

A makon jiya an kai hare-hare a wasu kauyuka na Mangu inda 'yan bindiga suka kashe gomman mutane, lamarin da ya sa gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita ta awa ashirin da hudu. Kafin haka, an rika kai jerin hare-hare da kashe-kashe a karamar hukumar musamman tun daga jajiberin Kirsimetin da ta gabata.

Sai dai Laftanar Janar Lagbaja ya umarni dakarunsa su "dauki karin matakai masu kaifi sannan ku kawar da 'yan ta'adda da ke yin barna a Filato da wasu jihohin," a cewar wata sanarwa da kakakin rundunar sojin kasa Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya fitar.

Sojin Nijeriya sun sha alwashin murkushe 'yan ta'adda da ke addabar Mangu./Hoto:Rundunar Sojojin Nijeriya

"Kada ku raga wa mutanen da ke hana zaman lafiya a Filato kuma ku kawar da duk wasu 'yan ta'adda da ke addabar jama'a da kona kayansu da hana gudanar da kasuwanci," in ji Laftanar Janar Lagbaja.

A nasa bangaren, gwamnan jihar Filato Caleb Mutfwang ya jinjina wa rundunar sojojin Nijeriya bisa zage dantsenta wajen ganin ta wanzar da zaman lafiya a jiharsa, yana mai cewa bai taba nuna shakku kan kokarin sojoji na kawar da masu tayar da yamutsi a jihar ba.

TRT Afrika