Hukumar kula da sufurin jiragen sama a Sudan ta ce ta tsawaita rufe sararin samaniyar kasar zuwa ranar 31 ga watan Yuli.
Hukumar ta bayyana haka ne a yau Litinin.
Sai dai ta ce za a ci gaba da barin jiragen da ke kai kayan agajin gaggawa da wadanda ke kwashe mutane daga kasar idan sun samu izini daga hukumomin filin jirgin saman Khartoum International Airport.
Wannan sanarwa na zuwa ne a yayin da mataimakiyar sakataren harkokin wajen Amurka a kan Afirka Molly Phee za ta kai ziyara Addis Ababa, babban birnin Ethiopia ranar Litinin don ganawa da shugabannin Afirka game da rikicin na Sudan.
Wata sanarwa da ma'aikatar wajen Amurka ta fitar ranar Lahadi ta ce "muna kira ga rundunar sojin Sudan (SAF) da dakarun Rapid Support Forces (RSF) su yi gaggawar kawo karshen rikicin sannan su koma barikin soji.
Haka kuma muna kira a gare su da su yi biyayya ga dokokin kasashen duniya, sannan su bayar da damar shigar da kayan agaji ga farar-hula ba tare da shamaki ba."
An rufe sararin samaniyar Sudan ne bayan yak ya kaure tsakanin rundunar sojin kasar da dakarun RSF a tsakiyar watan Afrilun da ya gabata.
Kawo yanzu an kashe akalla mutum 1,133 a rikicin, a cewar ma'aikatar lafiyar kasar, tana mai cewa yakin ya yi kamari a babban birnin kasar da yankin Kordofan da na Darfur, inda ya rikide ya zama rikicin kabilanci a Yammacin yankin.
Fiye da mutum miliyan 2.9 sun tsere daga gidajensu sakamakon yakin, ciki har da mutum kusan 700,000 da suka ketara zuwa kasashen da ke makwabtaka.