Hukumomi sun tsare jagoran 'yan hamayyar Senegal Ousmane Sonko ranar Juma'a sakamakon wata hatsaniya da ta kaure tsakaninsa da jami'an tsaron da aka jibge a kofar gidansa, wadda ta kai shi ga kwace wayar daya daga cikinsu.
Lauyoyin Sanko da kuma mai shigar da kara na kasar sun tabbatar da aukuwar lamarin.
Sonko, mai shekara 49, ya wallafa sako a shafinsa na X, wanda a baya ake kira Twitter cewa wasu sojoji da aka girke a kofar gidansa ne suka rika daukar bidiyonsa ba tare da saninsa ba lokacin da yake dawowa daga masallaci.
Ya kara da cewa bayan ya lura da abin da suke yi ne sai ya kwace wayar daya daga cikinsu sannan ya bukaci su goge bidiyon da suka dauka.
Hakan ne ya haifar da hatsaniyar da ta kai ga sake tsare shi.
Tsarewar da aka yi masa ba ta da nasaba da hukuncin da aka yanke wa Mr Sonko na daurin shekara biyu a kurkuku a watan Yuni bisa zargin bata tarbiyyar matasa - ko da yake har yanzu ba a kai shi gidan yari ba.
Ya musanta wannan zargi inda ya ce gwamnatin kasar ta dauki matakin ne domin hana shi yin takara a zaben shekarar 2024.
Tsarewar da aka yi masa a baya ta haifar da daya daga cikin munanan tarzoma da aka taba yi a Senegal, yayin da magoya bayansa suka yi arangama da jami'an tsaro, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.