Bishiyar ta girmi kusan duk wani abu mai rai a kauyen a cewar limanin Cocin St. Joseph Parish Binshua wanda ya ba da umarnin sare bishiyar. Hoto: CNA

An umarci a sare wata bishiya da ta shafe sama da shekaru 100 a kauyen Binshu da ke yankin Nkambe ta tsakiya a arewa maso yammacin Kamaru kan zargin tsafi da maita.

Limamin Cocin St. Joseph Parish Binshua, Fr. Anthony ne ya umarci Kiristocin ƙauyen su sare bishiyar saboda zargin tana ɗauke da maita kuma ana tsafi da ita, kamar yadda kafar yada labarai ta Kamaru CNA ta rawaito.

"Wannan bishiyar ta wuce shekara 150 da tsirowa, kuma ta kasance gida ga duk wani abu mai tsirowa daga kasa da dabbobi da kuma nau'ukan tsuntsaye da ƙwari da ke rayuwa a kan wannan bishiyar," a cewar Fr. Anthony.

‘’Irin wannan wuri kuma abu ne da Hukumar Kula da Ilimi da Kimiyya da Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO ke ayyana su a matsayin wuraren tarihi da suka cancanci kariya ta musamman, ba wai a lalata su ko a dinga camfa su ba," a cewar wani matashi mazaunin ƙauyen da ya bayyana damuwarsa game da wannan mataki.

Matashin ya ƙara da cewa, ''A wannan ƙarni na 21 da muke ciki, bai kamata a samu irin haka ba a daidai wannan lokacin da duniya ke fama da munanan illolin sauyin yanayi da kwararowar Hamada,'' in ji shi.

Rahotannin sun bayyana cewa bishiyar tana dashe ne kusa da cibiyar kiwon lafiya ta ƙauyen Binshua.

“Limamin cocin da mabiyansa sun yi ikirarin cewa bokaye da matsafa ne suke gudanar da ayyukansu na tsafi da bishiyar, inda suke haifar da tashe-tashen hankula da barna a ƙauyen," a cewar matashin.

Wasu mazauna ƙauyen sun dasa ayar tambaya kan dalilin da ya sa Fr. Anthony a matsayinsa na shugaban addini bai yi amfani da ikonsa na korar bokaye da matsafa ba, maimakon sare bishiyar, kamar yadda CNA ya bayyana.

Ra'ayoyin mutanen ƙauyen sun bambanta kan batun, wasu na adawa da matakin yayin da mabiyan limamin ke goyon bayansa.

Alamu sun yi nuni da cewa shugaban yankin da wasu dattawan ƙauyen sun ba da goyon bayansu kan sare bishiyar, kamar dai yadda wani da ya shaida lamarin ya bayyana wa CNA.

TRT Afrika