Rundunar ƴan sandan Nijeriya ta ce ta gurfanar da tauraruwar finafinan Kannywood Amal Umar a gaban kotu bayan ta yi yunƙurin bai wa wani jami'inta cin-hanci.
Ta bayyana haka ne a wani taron manema labarai da mai magana da yawun Rundunar Ƴan Sandan Nijeriya Shiyya ta Ɗaya da ke Kano CSP Bashir Muhammad da ya gabatar ranar Labara a birnin na Kano.
Ya ƙara da cewa ƴan sanda sun gufanar da "wata jarumar ƴar wasan Hausa wadda aka fi sani da Amal Umar mai shekara 24 a gaban kotu domin yunƙuri na bayar da cin-hanci da ta yi ga ASP Salisu Bujama wanda yake bincike kan wani batu na damfara da saurayinta ya yi wa wani Alhaji Yusuf Adamu ta N40m."
A cewar rundunar ƴan sandan, saurayin Amal ya karɓi kuɗin ne da zummar "za su yi kasuwancin waya, amma daga nan ba a sake ganinsa ba."
Bashir Umar ya ce daga nan ne lauyoyin Alhaji Yusuf suka shigar da ƙara a Rundunar Ƴan Sandan Nijeriya Shiyya ta Ɗaya da ke Kano, kuma Mataimakin Babban Sufeton Ƴan sanda Mamman Sanda ya yi umarni a gudanar da bincike .
Bincike ya gano cewa saurayin Amal ya tura naira miliyan goma sha uku a asusunta abin da ya sa ƴan sanda suka gayyace ta domin gudanar da bincike, in ji kakakin ƴan sandan.
Ya ƙara da cewa ita da kanta ta tabbatar da cewa saurayinta ne ya tura mata kuɗin, yana mai cewa "bayan an bayar da ita beli sai ta je kotu ta nemi a dakatar da binciken da ake yi mata."
"Da ma motarta tana nan ofishin ƴan sanda (Zone One). Bayan wani lokaci ta zo ta nemi a ba ta motarta, sai ta yi yunƙurin bai wa ɗan sanda, ASP Salisu Bujama cin-hanci na naira dubu ɗari don ya yi haƙuri ya kashe wannan magana kuma a ba ta motarta ta tafi da ita," a cewar CSP Bashir Umar.