Akalla mambobin coci 25 aka yi garkuwa da su a Jihar Ondo da ke kudu maso yammacin Nijeriya.
Kafafen watsa labaran kasar sun ruwaito wadanda suka shaida lamarin na cewa ‘yan bindigar sun yi garkuwa da mambobin a ranar Juma’a da rana a lokacin da suke hanyar zuwa jana’izar wani mamba na cocin.
Rahotanni sun ce a lokacin ne ‘yan bindigan suka tare mambobin cocin Christ Apostolic inda suka shige daji da su.
An ruwaito mai magana da yawun ‘yan sandan reshen Jihar Ondo Funmi Odunlami inda ta tabbatar da faruwar lamarin tare da cewa suna bincike tare da cewa tuni aka aika da jami’an tsaro domin ceto wadanda aka sace.
Ko a bara sai da wasu ‘yan bindiga suka kashe masu ibada a wata coci 40 tare da raunata jama’a a da dama. Sai dai wasu na ganin adadin wadanda aka kashe a lokacin harin ya zarta 40.