Hukumomin mulkin soja a Nijar sun rusa majalisun ƙananan hukumomi 266 da ke faɗin ƙasar da kuma shugabannin majalisun jihohi takwas waɗanda tuni aka maye gurbin su da wasu wakilai na musamman wato administrateurs délégué.
An bayyana haka ne a wata sanarwa da aka karanto a gidan talbijin na ƙasar ranar Alhamis da daddare.
"An rusa majalisun ƙananan hukumomi da kansiloli da wakilan larduna," in ji sanarwar ba tare da bayyana dalilin ɗaukar matakin ba.
An maye gurabensu da jami'an soji da na ƴan sanda da wasu ma'aikatan gwamnati.
Shugaban mulkin sojin ƙasar Janar Abdourahamane Tiani ne ya sanya hannu a kan dokar da ta rusa majalisun ƙananan hukumomin da na larduna, in ji gidan talbijin na Tele Sahel.
Shugabannin da aka rusa zaɓaɓɓu ne kuma kundin tsarin mulkin Nijar ya ba su wa'adin shekaru bakwai na jagorancin ƙananan hukumomin.
Kazalika an sauke magajin birnin Yamai, Oumarou Dogari, daga kan muƙaminsa inda aka maye gurbinsa da wani kanar na soji.
A makon jiya ma'aikatar Ministan Cikin Gida da Ayyukan Ƙananan Hukumomin ke ƙarƙashin kulawarta ta haramta wa shugabannin ƙananan hukumomin kashe kuɗaɗe sai dai abin da ya shafi biyan albashin ma'aikata.
A watan Yulin da ya gabata ne sojoji suka yi wa gwamnatin farar-hula ta Mohamed Bazoum juyin mulki lamarin da ya sanya ƙungiyar ECOWAS ta dakatar da ƙasar daga cikinta.