Hukumar da ke Kula Kafafen Yada Labarai a Kamaru (NCC) ta dakatar da tashar talabijin ta CANAL Plus International daga yaɗa shirye-shiryenta bayan da ta yaɗa wani shiri da ke "tallata luwaɗi" a faɗin ƙasar, kamar yadda Shugaban Hukumar Joseph Chebongkeng Kalabuse ya tabbatar.
Ya bayyana hakan ne kwana hudu bayan hukumar NCC ta rubuta wasiƙa ga tashar talabijin ɗin kan yadda ta saɓa wa gargadin da aka yi mata a watan Yunin shekarar 2023, kuma ta buƙaci tashar da ta dakatar da yaɗa shirin.
An yi amannar cewa tashar tana yaɗa abubuwan 'yan luwaɗi da maɗigo da batsa ga al'ummar Kamaru.
Joseph Chebongkeng ya ce dakatar da tashar ya fara aiki ne daga ranar 25 ga watan Satumba, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar Kamaru ya bayyana.
"Idan muka lura cewa sun ci gaba da yada abin da suke yi, dakatarwar za ta ci gaba har sai sun sauya," kamar yadda ya yi gargadi.
Shugaban hukumar ya ce hukumar ta dauki matakin ne bisa la'akari da sashe na 346 na kundin dokokin Kamaru . "Muna aiki da doka ne kawai kuma akwai bidiyon batsa da su ma aka haramta su," in ji shi.