Nijeriya na amfani da jiragen yaki wajen fatattakan barayin daji:Hoto/Facebook/Nigeria Air Force HQ

Kasa da kwana daya bayan Hafsan Hafsoshin Sojin Nijeriya Janar Christopher Musa ya bukaci dakatun kasar da su fatattaki 'yan bindiga, an kashe 'yan bindiga fiye da 100 bayan wani hari da aka kai ta sama a yankin Arewa-maso Yammacin Nijeriya.

Kafar yada labarai ta PR Nigeria ta ruwaito cewa an yi wani aikin hadin gwiwa na soji bayan da aka samu sahihan bayanan sirri a wasu wurare da 'yan bidigar suke buya a yankunan jihohin Kebbi da Zamfara.

Yayin kai musu farmakin, an samu hadin gwiwa tsakanin dakarun sojin sama da na kasa, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

“Kwamandan Rundunar Hadarin Daji ya ce sun yi nasarar kawar da 'yan ta'adda da dama da shugabanninsu a yankin Sangeko da Karamar Hukumar Maru a jihar Zamfara.

"An gano 'yan bindigar ne bayan samun wasu bayanan sirri daga wurare daban-daban da kuma shirinsun na nausawa yankunan jihar Neja. 'Yan ta'addan suna tafiya a ayarin babura da yawa a hanyar garin Kabaro zuwa Sangeko.

"Bayan haka an kai wa 'yan ta'addan hari ta sama inda aka kawar da dama daga cikinsu. Haka zalika an lalata babura".

Mai magana da yawun Rundunar Sojin Saman Nijeriya Air Commodore Edward Gabkwet ya tabbatar da faruwar al'amarin ga kafar yada labarai ta PR Nigeria. Sai dai bai yi karin haske ba kan adadin mutanen da suka mutu ko jikkata ba sanadin farmakin.

"Farmakin da aka kai a yankin ya samu nasara sosai, sai dai ba zan iya cewa komai ba dangane da alkaluma saboda farmaki ne da ake ci gaba da yi," in ji shi.

A ranar Talata yayin da ya kai ziyara Maiduguri, Hafsan Hafsoshin Sojin Nijeriya Janar Christopher Musa ya bukaci dakarun kasar da kada su rika jira sai 'yan Boko Haram sun kai musu hari kafin su tunkare su.

TRT Afrika