Darakta Janar na WHO a ranar 8 ga Satumban 2024 ya bayyana cewa kusan rabin jama'ar Sudan su miliyan 25 na buƙatar taimakon gaggawa. / Hoto: AA

Sama da mutane 20,000 aka kashe a rikicin Sudan da ake ci gaba da yi tun watan Afrilun 2023 tsakanin sojoji da mayakan RSF, in ji Darakta Janar na Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) a ranar Lahadin nan.

Da yake bayani ga 'yan jarida a garin Port Sudan a yayin ziyarar kwanaki biyu a Sudan, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce an raba sama da mutane miliyan 10 da matsugunansu, baya ga wasu mutanen miliyan biyu da suka gudu zuwa ƙasashe makota.

Ya ce "Yanayin bukatar agajin gaggawa na da firgitarwa, a yayin da ba a daukar matakan da suka kamata na kawo karshen rikicin da kuma rage raɗaɗin da ya janyo."

Ya kuma ce kusan rabin jama'ar Sudan su miliyan 25 na bukatar agajin gaggawa, inda kashi 70 na Sashen Kula da Lafiya a Ƙasar ba ya aiki.

'Ku farka ku taimaki Sudan'

Jagoran na WHO ya yi kira ga ƙasashen duniya da su farka tare da fitar da Sudan daga wannan mummunan yanayi da take ciki.

A ranar Asabar, Ghebreyesus ya jaddada ƙudirin WHO na ƙoƙarin magance ƙalubalen kula da lafiya da bayar da agajin jin ƙai a Sudan, ciki har da rashin tsaro da tsugunar da ɗimbin jama'a da ambaliyar ruwa da kuma ɓarkewar cututtuka.

TRT Afrika