An kai wa Jakadan Kungiyar Tarayyar Turai a Sudan hari a gidansa da ke Khartoum a ranar Litinin /Hoto: AA

Fadan da ake yi tsakanin dakarun gwamnati da na bangaren adawa a Sudan ya yi sanadin mutuwar kusan mutum 200 tare da jikkata 1,800.

Sannan an lalata asibitoci da kawo tsaiko ga harkokin jin kai a ranar Litinin, bayan shafe kawana uku ana gwabzawa.

An shafe makonni ana ja-in-ja a kan samun karfin iko tsakanin dakarun manyan janar din biyu da suka yi juyin mulki a 2021; shugaban gwamnatin sojin Sudan, Abdel Fattah al Burhan da mataimakinsa Mohamed Hamdan Daglo, wanda ke jagorantar dakarun RSF.

An kai wa Jakadan Kungiyar Tarayyar Turai a Sudan hari a gidansa da ke Khartoum a ranar Litinin, a cewar Josep Borrell babban jami'in diflomasiyyar kungiyar.

Wani mai magana da yawun kungiyar ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP cewa "ba abin da ya samu jakadan sakamakon harin.

"Alhakin hukumomin Sudan ne su samar da tsaro a wuraren da jami'an diflomasiyya suke, kuma hakan na kunshe a cikin dokar kasa da kasa," in ji Borell.

Ana ci gaba da yakin a mafi yawan sassan kasar tare da fargabar cewa zai iya yaduwa zuwa sauran yankunan.

Mazauna kasar na cike da fargaba da tsoro yayin da suke azumtar kwanaki goman karshe na watan Ramadan suna kallon tataburzar da ake yi daga tagogin gidajensu.

Ana ta kai hare-haren sama da jefa rokoki da harbe-harben bindiga ta kowane sako.

Mutane na ta bin dogwayen layuka don sayen burodi da man fetur a wuraren da ba a kai ga rufewa ba. Kazalika ana ta fama da katsewar wutar lantarki.

Volker Perthes, wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ya shaida wa Kwamitin Tsaro na MDD a wani taron sirri cewa, an kashe a kalla mutum 185 tare da jikkata 1,800 zuwa yanzu.

"Lamari ne mai sarkakiya don haka zai yi wahala a iya gane wa yake da nasara zuwa yanzu," Perthes ya shaida wa manema labarai bayan kammala taron.

Tun da fari a ranar Litinin, shugaban MDD Antonio Guterres ya sake yin kira ga bangarori biyu masu fada da juna a Sudan da su tsagaita wuta. Ya yi gargadi cewa ci gaba da yakin ka iya tabarbarar da al'amura a kasar da ma yankin baki daya."

An dakatar da kai agaji

Da farko ma’aikatan lafiya a Sudan sun ce fararen hula 100 aka kashe da kuma gomman sojoji daga bangarorin biyu, amma ana tsammanin yawan ya zarce haka sosai, inda mutane da dama da suka jikkata har suka kasa zuwa asibiti.

Kungiyar likitoci ta yi gargadi cewar fadan ya lalata asibitoci da dama a Khartoum da sauran birane, inda wasu ma suka tsaya da aiki baki daya.

Hukumar Lafiya ta Duniya tuni ta yi gargadi cewa jinin da ake saka wa marasa lafiya da yawa daga cikin asibitoci tara da ke Khartoum ya kare, sannan babu wasu muhimman kayan aiki.

A Darfur da ke yankin yammacin kasar kuwa, Kungiyar Likitoci ta MSF ta ce an kai mutum 136 da suka jikkata asibiti daya tilo na El Fasher da har yanzu yake aiki a Jihar Arewacin Dafur.

“Mafi yawan wadanda suka jikkatan fararen hula ne da fadan ya rutsa da su – kuma a cikin su akwai yara da dama,” in ji Cyrus Paye na kungiyar MSF.

“Mutum 11 sun mutu sakamakon raunukan da suka ji a cikin sa'a 48 na farkon yakin, saboda rashin kayan aiki,” ya ce.

Ma’aikatan Hukumar Shirin Abinci ta MDD na daga cikin wadanda suka rasa rayukansu a ranar Asabar a Darfur, inda aka dinga sace kayan abinci da na lafiya na ayyukan agaji a wajen, a cewar kungiyoyin Save the Children da MSF.

Kungiyoyi da dama sun dakatar da ayyukansu na wucin gadi a kasar, inda kashi daya bisa uku na al’ummar ke bukatar ayyukan agaji.

“Wannan fadan ya ruruta matsalar da dama can akwai ta a kasa, tare da tursasa wa hukumomin MDD da sauran abokan huldarmu na agaji su dakatar da ayyukansu fiye da da 250 a Sudan,” a cewar jagoran samar da agaji na MDD, Martin Griffiths.

TRT World