Rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Kano ta sanar da cewa ta kama mutum uku da wayoyi 318 wadanda take zargin na sata ne.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana haka a wani sako da ya wallafa a shafin sada zumunta ranar Asabar.
SP Kiyawa ya bayyana cewa tun da farko wani Muhammad Adam da wasu mutum tara ne suka kai musu korafi kan cewa da tsakar dare barayi sun fasa musu shaguna a kusa da filin wasa na Sani Abacha inda suka sace wayoyi 671.
A cewarsa, daga nan ne ‘yan sanda suka soma bincike wanda har ya kai ga kama mutanen uku inda mutanen suka amince da sace wayoyin.
Sai dai wadanda ake zargin sun shaida wa ‘yan sandan cewa tuni suka sayar da wasu daga cikin wayoyin.
Rundunar ‘yan sandan ta bayyana cewa za a gurfanar da mutum ukun a gaban kotu da zarar an kammala bincike.
Ko a kwanakin baya sai da ƴan sandan a Kano suka ce sun ƙwato wayoyi 890 daga hannun wasu matasa biyu da ake zarginsu da satarsu.