'Yan sandan sun ce har yanzu akwai sauran mutum guda da suke nema wanda ake zargi. Photo/Ghana Police

‘Yan sanda a kasar Ghana sun ce sun kama mutum shida wadanda suke zargi da far wa jami'insu a bakin aiki.

A wata sanarwa da mataimakiyar kwamishinar ‘yan sanda a kasar bangaren watsa labarai ta fitar, ta ce lamarin ya faru ne a wani shingen bincike da ke gundumar Kumawu a yankin Ashanti.

Grace Ansah-Akrofi ta bayyana cewa wadanda ake zargin sun hada da Edward Boateng da Evans Addo da Yaw Kusi da Michael Owusu da Yaw Boateng da Emmanuel Mensah da kuma wani mutum daya da har yanzu ake nemansa ruwa a jallo.

Ta bayyana cewa duka wadannan mutanen sun cika mota tasi lamarin da ya sa daya daga cikin ‘yan sanda ukun da ke aiki a shingen binciken ya tsayar da su tare da bukatar duba motar.

“A yunkurinsu na hana a duba motar sai suka dirar masa inda suka soma dukansa.

“Karin ‘yan sandan da aka tura domin shawo kan lamarin sun yi nasarar cafke mutum shida cikin wadanda ake zargin,” in ji Grace.

Ta kara da cewa dan sandan ya ji rauni a gwiwarsa haka kuma daya daga cikin wanda ake zargin shi ma yaji rauni kuma tuni aka aika da su asibiti.

Sai dai ta ce sauran ‘yan sandan wadanda suna wurin aka far wa abokin aikinsu an dakatar da su daga aiki inda tuni aka mika su ga sashen kula da kwarewa da ɗa’ar ma’aikatan ‘yan sanda domin gudanar da bincike.

Ko a farkon watan nan sai da rundunar 'yan sandan Ghana ta ce ta kama mutum hudu da ake zargi sun ci zarafin wani jami'inta.

Wadanda suka ci zarafin nasa sai da suka lakada wa dan sandan duka har suka ci karfinsa suka kwace bindiga da wayoyinsa.

TRT Afrika da abokan hulda