An sace 'yan matan shida ne da mahaifinsu ranar 2 ga watan Janairun 2024. Hoto/ NPF

Rundunar ƴan sandan Nijeriya ta tabbatar da kama wani ɗan bindiga wanda ake zargi da kashe matashiyar nan Nabeeha da kuma garkuwa da wasu.

Rundunar ta tabbatar da hakan ne a wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi inda ta ce ta kama ɗan bindigar a wani otel da ke garin Tafa a hanyar Abuja zuwa Kaduna.

A sanarwar, ta ce ɗan bindigar mai shekara 28 mai suna Bello Mohammed asalin ɗan jihar Zamfara ne kuma an kama shi da zunzurutun kuɗi har naira miliyan 2.25, inda ake zargin kuɗin fansa ne da ya karɓa.

“Wanda ake zargin a lokacin da ake yi masa tambayoyi, ya tabbatar da cewa yana daga cikin gungun waɗanda suka yi garkuwa da wani Barista Ariyo a unguwar Bwari da ke Abuja a ranar 2 ga watan Janairun 2024, inda suka kashe wasu daga cikin wadanda suka yi garkuwa da su, daga ciki har da Nabeeha, wadda ƴa ce ga lauyan, a ranar 13 ga watan Janairun 2024 a sansanin masu garkuwan da ke Jihar Kaduna.

"Wanda ake zargin, a cikin wani yanayi mai ban mamaki, ya bayar da naira 1,000,000 (Naira miliyan daya kacal) don jawo hankalin DPO, wanda ya ki amincewa da tayin, inda ya gudanar da aikinsa yadda ya kamata," in ji sanarwar.

A makon da ya gabata ne runduna ƴan sandan Nijeriya ta tabbatar da kuɓutar da ƴan uwan Nabeeha waɗanda ke hannun ƴan bindiga.

An sace 'yan matan shida ne da mahaifinsu ranar 2 ga watan Janairun da muke ciki a gidansu da ke Bwari a Abuja.

Sai dai daga bisani 'yan bindigar sun saki mahaifinsu sannan suka bukaci ya nemo N60m a matsayin kudin fansa.

TRT Afrika