Sojojin Nijeriya sun ce suna ci gaba da kakkabe sauran mayakan da ke ikirarin Jihadi a arewa maso gabashin Nijeriya, bayan mutuwar shugabansu Abubakar Shekau./Hoto:AFP

Wasu mayakan kungiyoyin da ke ikirarin jihadi sun kashe akalla mutum 15 a hare-haren da suka kai a kauyuka biyu da ke kusa da Chibok da ke jihar Borno a arewacin Nijeriya, a cewar mazauna yankin ranar Laraba.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato wasu mazauna yankin suna cewa ‘yan bindiga a cikin motocin a-kori-kura da kan babura dauke da manyan bindigogi sun kai hari a kauyukan Gatamarwa da Tsiha ranar Litinin, inda suka kashe mutanen tare da kona gidajensu bayan sun sace kayan abinci.

"Mutum 15 ne suka mutu sakamakon hare-haren da aka kai a kauyukan biyu," in ji Manasseh Allen, shugaban kungiyar Ci-gaban Yankin Chibok (CADA), a hira da AFP.

Babu cikakken bayani game da ko mayakan Boko Haram ne suka kai harin ko kuma abokan adawarsu na kungiyar ISWAP.

Maharan, sanye da kakin sojoji, sun shiga kauyen Gatamarwa, inda suka bude wuta kan mutane, ciki har da masu zaman makoki jim kadan bayan sun dawo daga wata jana’iza, a cewar Allen.

"Maharan sun kashe mutum 12 a kauyen Gatamarwa sannan suka kashe mutum uku a Tsiha," in ji shi.

Wasu mutum biyu sun tabbatar da wannan bayani na Allen.

"Bayan kase-kashen, maharan sun kwashi kayan abinci sannan suka cinna wuta a kayukan biyu," in ji Ayuba Alamson, wani dattijo a Chibok, yana mai tabbatar da adadin mutanen da aka kashe.

Kazalika maharan sun sace wata budurwa a Tsiha, in ji wani mazaunin kauyen mai suna Smson Bulus.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Borno Nahum Daso ya tabbatar da kai hare-haren, amma ya ki yin karin bayani game da adadin mutanen da aka kashe.

Chibok ya ja hankalin duniya a 2014 lokacin da mayakan Boko Haram suka sace mata 'yan makarantar-kwana fiye da 200.

AFP