Shekara ɗaya bayan ɓarkewar yaƙi Sudan, Alabaki Abbas Ishag mai shekara 24, yana rayuwa a sansanin ƴan gudun hijira da ke Chadi da ke makwabtaka.
Ishag yana cikin mutum miliyan 8.5 da yaƙin da ke gwabzawa tsakanin sojojin Sudan da dakarun RSF ya raba da muhallansu.
Ya isa ƙauyen Koufroun na Chadi da ke kan iyaka bayan ya kwashe shekara ɗaya yana ɓuya -- da zummar tsere wa hare-haren da ake kai wa a yankin Darfur da ke yammacin ƙasar.
Ya yi ta ɓuya a cikin gine-gine da aka lalata a yankin El-Geneina, babban birnin Yammacin Darfur.
Yaƙi ya ɓarke ne ranar 15 ga watan Afrilu tsakanin sojojin Sudan ƙarƙashin jagorancin Janar Abdel Fattah al-Burhan da dakarun kai ɗaukin gaggawa na Rapid Support Forces (RSF) da ke ƙarƙashin tsohon mataimakinsa Mohamed Hamdan Daglo.
Babban hatsari
A El-Geneina kaɗai, an kashe tsakanin mutum 10,000 zuwa 15,000 a watanni tara a farkon yaƙin, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.
Rundunar RSF "ta yi yunƙurin ɗauka ta a matsayin soja domin na taya ta kai hare-hare, amma bayan da na ƙi bin umarninta sai ta sanya ni a cikin jerin mutanen da za ta kashe", in ji Ishag.
"Ina kallo suna jefa mutanen da na sani a cikin manyan ƙaburbura suna binne su da ransu.''
Ishaq ya isa garin Koufroun, inda ya yi saye da sayawar don samun na kashewa. Hakan ya ba shi damar cin abinci aƙalla sau ɗaya a kowace rana.
Sai dai yana cike da fargaba sakamakon matsowar damuna.
Cunkoso a sansanin ƴan gudun hijira
"Ba ni da kuɗin da zan gina wa kaina gida," in ji Ishag, yana mai nuna tabarmar da ya yi amfani da ita wajen yin rufi a dakin da yake kwana a sansanin Koufroun inda ƴan gudun hijira fiye da 9,100 suke samun mafaka, a cewar MDD.
Yanzu ƴan gudun hijirar Sudan kimanin miliyan ɗaya suna zaune a Chadi -- ita ce ƙasar da ta fi yawan ƴan gudun hijirar Sudan.
A cikin shekara ɗaya da ta wuce, ƴan gudun hijirar Sudan sama da 571,000 suka je Chadi ta ƙasa, ƙari a kan fiye da mutum 400,000 da suka shigar ƙasar sakamakon yaƙin da aka yi a Darfur a 2003.
Ƴan gudun hijira sama da 160,000 suke tsugune a sansanin Adre da ke kan iyala, wanda shi ne wuri na farko da mutum zai isa idan ya tsallaka iyaka.
Hada Ishag Fadallah ta isa Adre tare da ƴayanta bakwai a farkon watan Nuwamba.
Babban bala'i
"Dakarun RSF sun zo gidanmu inda suka harbe mijina sannan suka sace duk abin da muka mallaka, kuma wasu daga cikinsu sun doke mu," a cewar Ishag, mai shekara 56.
Mata da ƙananan yara su ne kusan kashi 90 na ƴan gudun hijirar Sudan da suka isa Chadi a cikin shekara ɗaya da ta gabata, in ji MDD.
A watan da ya gabata, Hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP) ta yi gargaɗi cewa za ta dakatar da tallafin abinci ga ƴan gudun hijirar Sudan da ke Chadi a watan Afrilu saboda ƙarancin kuɗi, inda ta yi kira a ba ta taimakon ƙarin kuɗaɗe domin kauce wa faɗawa cikin "babban bala'i".