Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta tabbatar da rushewar wani gini a unguwar Sabon Lugbe a Abuja babban birnin ƙasar.
Rundunar ‘yan sandan ta bayyana cewa binciken da ta gudanar na wucin-gadi ya nuna cewa a baya hukumar gudanarwa ta birnin tarayya ta taɓa rushe ginin sakamakon an gina shi a wurin da bai dace ba.
Sai dai ta bayyana cewa bayan haka ‘yan jari-bola waɗanda ke neman ƙarafa sun ƙara lalata ginin wanda hakan ya ja ya ƙara rushewa.
‘Yan sandan sun bayyana cewa babu wanda ya rasa ransa haka kuma akwai mutum biyar waɗanda ɓaraguzan ginin suka danne su amma dukansu an ceto su.
Ana yawan samun matsalar rushewar gini a Nijeriya musamman Abuja babban birnin ƙasar.
Ko a kwanakin baya sai da wani gini mai hawa biyu ya rufta a unguwar Kubwa da ke Abuja.
Haka kuma a kwanakin baya ma mutane da dama sun maƙale bayan wani ginin otel mai hawa huɗu ya rushe a unguwar Garki da ke Abujar.
Kawararu suna yawan cewa manyan matsalolin da ke jawo rushewar gini sun hada da amfani da kayan gini marasa inganci da rashin aiki mai kyau da rashin tuntubar kwararru a harkar gini da rashin bin ka'idojin gini da rashin saka tubali mai kyau, da sauran su.